Bankuna za su fara bayar da katin dan kasa mai hade da na ATM — Pantami

0
103

Gwamnatin TarayyaTarayya ta ba wa bankunan kasuwanci izinin fara ba wa abokan huldarsu katin cirar kudi na ATM da ke hade da katin shaidar dan kasa a wuri guda.

Ministan Sadarwa mai barin gado, Isa Ali Pantami, ya sanar cewa Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince bankuna su fara bayar da katin na bai-daya ba tare da sun caji kwastomomi ko sisi a kan kudin katin ATM da aka saba ba.

“An ba wa bankuna izinin buga katunan Mastercard ko Visa da za su yi amfani a matsayin katin shaidar dan kasa ba tare da sun caji ’yan Najeriya karin kudi ba.

“Duk mai son karbar katin banki, sai ya sanar da su cewa mai hade da katin dan kasa yake so, sai su ba shi kati daya da ya hade abubuwa biyun,” in ji Pantami.

Ya bayyana cewa, Hukumar Kula da Shaidar Dan Kasa (NIMC) ta yi haka ne da hadin gwiwar Babban Bankin Najeriya (CBN) “domin saukaka wa duk mai bukata samun katin dan kasa ta hannun bankinsa.”

Da yake jawabi bayan zaman karshe na Majalisar Zartarwa ta Tarayya da gwamnatin Buhari ta gudanar, a Fadar a Shugaban Kasa ministan, Pantami ya bayyana cewa Dokar NIMC ta 2007, ta wajabta wa ’yan Najeriya mallakar lambar shaidar dan kasa (NIN) ne kawai.

Ya ci gaba da cewa, “A lokacin mallakar katin shaidar ba dole ba ne, ra’ayi ne; Amma sai mutane suka rika kai wa NIMC korafi cewa ba su samu katinsu na dan kasa ba.

“A kan haka ne a shekarar 2022 muka fito da katin shaidar dan kasa na zamani, wanda mutun zai iya saukewa a wayarsa, wanda kuma ke amfani ba lallai sai mutum ya buga shi a takarda ba.

“Duk da haka aka ci gaba da samun korafi, musamman daga mazauna yankunan karkara, cewa suna bukatar rike katinsu na dan kasa a hannu.

“Shi ya sa muka saukaka samun katin, inda NIMC da bankin CBN suka yi hadin gwiwa domin tabbatar da ganin mutane za su iya zuwa bankunansu su karbi katin dan kasa mai hade da ATM.”

Sai dai bai fayyace lokacin da bankunan za su fara bayar da katin na bai-daya ba.

Idan za a iya tunawa a baya CBN ya sanar da shirinsa na bullo da katin cirar kudi a banki na bai-daya, wanda mutum zai iya cirar kudi daga asusun ajiyarsa da ke bankuna daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here