Buhari ya mikawa Tinubu lambar girma ta GCFR

0
101

Shugaban kasa Muhammadu Buhari mai barin gado, ya baiwa shugaban kasa mai jiran gado Asiwaju Bola Tinubu lambar girma ta kasa (GCFR).

Buhari ya karrama Tinubu ne a wajen taron da aka gudana a Abuja ranar Alhamis.

Wannan karramawar ta GCFR ta zo ne a wani bangare na Bikin mika mulki ga zababben shugaban kasa da mataimakinsa, Kashim Shettima.

Idan za’a iya tunawa cewa Buhari ya bayyana aniyarsa ta mika mulki nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.

Shugaba Buhari sai zai mika mulki a ranar Litinin mai zuwa, 29 ga Mayu, ga zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here