Kotu ta ci tarar dan takarar da ya nemi hana rantsar da Tinubu naira miliyan 40

0
129

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta ci tarar Naira miliyan 40 ga tsohon dan takarar shugaban kasa, Ambrose Owuru, kan karar da ya shigar na neman a dakatar da bikin rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa.

Wani kwamitin alkalai uku karkashin jagorancin mai shari’a Jamil Tukur, ya umurci Owuru ya biya shugaban kasa Muhammadu Buhari, da babban lauyan gwamnatin tarayya da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar INEC da Tinubu, da ya biya naira miliyan 40.

Mai shari’a Tukur ya bayyana cewa Owuru ya wahalar da bangaren shari’ar wajen gaza gabatar da kwararan shaidu da kuma tunzura wadanda ake kara.

Kotun daukaka kara ta ce korafe-korafen da Owuru ya yi kan zaben shugaban kasa na 2019 ba bakon abu ba ne.

Mai shari’a Tukur ya ce matakin da Owuru ya dauka na farfado da shari’ar da ta mutu a shekara ta 2019 a kotun koli na da nufin sanya matakan kananan kotuna su yi karo da babbar kotun koli.

A ranar 19 ga watan Mayu ne kotun daukaka kara ta kebe karar domin yanke hukunci bayan sauraron bayanan lauyoyin da suka gabatar a kan lamarin.

Tun da farko, lauya ga Tinubu, Adelani Ajibade, ya roki kotun daukaka kara da ta ci gaba da yanke hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar 11 ga watan Oktoban 2019.

Shi ma Lauyan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasar INEC, Hassan Aminu, ya bukaci kotun daukaka kara da ta yi watsi da bukatar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here