Masana kimiyya sun samo wata hanyar yaƙi da ƙwayoyin cuta da ba sa jin magani

0
57

Masana kimiyya sun yi amfani da fasahar kwaikwayon dabi’ar dan adam wato AI wajen samar da wani sabon rigakafi da ka iya kashe kwayoyin cuta na Superbug, da ke kangarewa magunguna.

Masu binciken a Amurka da Canada sun yi amfani da fasahar ta AI wajen gano sinadaran da ka iya yi wa kwayoyin cutar da ba sa jin magani kwaf daya.

Gwaje-gwaje a dakunan gwajin magunguna ne suka kai ga samar da sabon maganin mai suna Abaucin, wanda yanzu haka ake kan aikin tantancewa kafin fara amfani da shi a kan jama’a.

Wakilin BBC ya ce Masana kimiyyar sun ce fasahar ta kwaikwayon dabi’ar dan Adam ta AI, na iya taimaka wa wajen hanzarta gano sabbin magunguna a yayin da ƙwayoyin cuta da dama ke ci gaba da turjewa magungunan da ake da su a yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here