Kwararru sun shawarci Neymar ya gaggauta ficewa daga PSG

0
131

A wani sabon yinkurin neman ficewarsa, Neymar bai taba gardamar ra’ayin ficewa da ga Paris Saint-Germain Bayan ga soke-soke da dama da ya fuskanta, da ma, suka hada na magoya bayan kungiyar ta birnin Paris.  Tuni dai, kwararen mai nazarin wasannin nan Emmanuel Petit, ya shawarci dan Barazil din, da ya kauce da gaggawa.

Komai ke faruwa dai daga karshe Neymar zai bara, ma’ana “idan ya ruba zai yi wari” .

Dan wasan da ya jima da kulla kawance da rayuwar jin dadi a birnin na Paris, na shirin tattara nasa ya nasa ya fice daga kungiyar ta Paris Saint-Germain a wannan kaka.

Dalilin fusatar Neymar dai baya rasa nasaba ne: lura da riritawa da kuma muhimmancin da kungiyar ke nunawa abokin  buga kwallonsa, Kylian Mbappé.  Bugu da kari, caccakar da magoya bayan kungiyar ta PSG ke yi masa, da ta kai zanga zanga har  gidansa.

Wanda hakan ne ke zama mabudin kofar ficewarsa daga kungiyar, kamar yadda  Emmanuel Petit ya shawarce shi da yi tun ya na da sauran mutuncinsa.  Daga karshen  dai M Petit ya ce, ba a kyauta wa tsohon dan wasan na FC Barcelone ba, kuma bai dace da irin wannan sakamako ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here