An kama uba ya yi wa ’yar sa mai shekara 5 fyade

0
116
CHICAGO, ILLINOIS - OCTOBER 19: Chicago police officers patrol downtown as the city celebrates the Chicago Sky's WNBA title on October 19, 2021 in Chicago, Illinois. The city has started to place police officers on unpaid leave for refusing to comply with the city's requirements that they report their COVID-19 vaccination status. Only about 65 percent of the city's police have complied with the order. (Photo by Scott Olson/Getty Images)

Wani magidanci da ya yi wa ’yarsa mai shekara biyar a duniya fyade ya shiga hannun ’yan sanda.

Rundunar ’yan sanda a jihar Ogun ta kama magidancin mai shekara 28 ne bayan mahaifiyar yarinyar da aka sakaya sunansu ta kai karar mijin nata zuwa ofishin ’yan sanda

Kakakin rundunar, SP Abimbola Oyeyemi, ya ce mahaifiyar yarinyar ce ta kai kara caji ofis bayan ta lura yarinyar tana jin zafi a matucinta a duk lokacin da take yin fitsari ko ake yi mata wanka idan aka taba gabanta.

Hakan ne ya sa ta tistiye ’yar, wadda ta sanar da ita cewa mahaifinta ne ya kwanta da ita a lokacin da mahaifiyar ta fita unguwa.

Samun wannan korafi ya sa babban jami’in ’yan sanda (DPO) na Ijebu-Mushin ya tura jami’ansa suka kamo mutumi a ranar 22 ga watan nan na Mayu, kuma bai musanta yin lalata da ’yar tasa ba.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Ogun, Olanrewaju Oladimeji ya bayar da umarnin a tura mutumin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) domin ci gaba da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here