Buhari ya yi wa magajinsa rakiya wasu wurare na fadar shugaban kasa (Hotuna)

0
81

Yayin da ya rage kwanaki uku a rantsar da zababben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, shugaba mai barin gado, Muhammadu Buhari, ya zagaya da shi lungu da sako na fadar shugabancin kasar, gabanin karbar ragamar mulkin kasar.

Wannan na zuwa ne kwana guda, bayan mataimakin shugaban kasar mai barin gado, farfesa Yemi Osinbajo, ya yi makamanciyar wannan rakiya ga Kashim Shettima, wato mataimakin zababben shugaban kasar.

Tuni dai shugaban kasar mai barin gado da mataimakinsa, suka fice daga gidajen da suke zaune a ciki a fadar Villa.

Haka zalika, dukkanin mukarraban shugaba Buharin, sun yi nisa da fara kwashe kayayyakinsu, yayin da ssuke bankwana da fadar ta Villa.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023, zabababben shugaban kasar, zai karbi rantsuwar karbar ragamar jagorancin Najeriya, tare da mataimakinsa Kashim Shettima,  Borno.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here