Ƙalubalen da ke gaban sabuwar gwamnatin Kaduna

0
54

A jihar Kaduna wacce Mallam Nasir El-Rufai zai mika mulki ga sabon zababben gwamna Sanata Uba Sani, akwai kalubale da dama wadanda sabon gwamnan zai tarar.

Dr. Tukur Abdulkadir, masanin siyasa ne a jami’ar jihar Kaduna KASU kuma ya ce duk da kokarin da gwamna mai barin gado Nasir El Rufai ya yi wajen saita al’amura a jihar Kaduna, akwai aiki a gaban sabon gwamna Uba Sani kuma zai gaji matsaloli da suka hada da;

Rashin tsaro

Dr. Tukur ya ce rashin tsaro matsala ce da ke ciwa al’ummar jihar Kaduna tuwo a kwarya musamman kudancin jihar.

“Garkuwa da jama’a ya na ci gaba da ta’azzara musamman a kauyuka da kuma sauran garuruwa da ke nesa da fadar jihar, dole ne sabon gwamna ya fito dqa tsare-tsare wadanda za su kawo karshen sace mutane domin su samu damar walwala a yankunansu” acewar Dr. Tukur.

Ya kuma kara da cewa jihar na fama da matsalar bangaranci da rikicin addini da kuma na kabilanci wadanda ke kara kawo rashin tsaro.

“Dole a takawa wannan abun birki saboda hada kan mutane sannan a samu zaman lafiya, duk da yake gwamnati mai barin gado tayi iyta kokarinta wajen magance hana tashe-tashen hankula to amma akwai bukatar sabuwa ta kara kaimi” in ji masanin siyasar.

Magance talauci da samar da aiki.

Fatara na daya daga cikin matsalolin da Uba Sani ya kamata ya magance a matsayinsa na sabon gwamna sannan ya samar da aiki ga dumbin matsa da ke jihar.

Dr. Tukur ya ce dole ne a farfado da masana’antu da Allah ya baiwa jihar Kaduna saboda za su samar da dubban ayyuka ga mutane da kuma hanyar samun abinci da kudaden shiga.

Har’ilayau, ya kara da cewa “inganta harkar noma tilas ne domin a mayarda manoma gonakinsu,a basu takin zamani sannan a magance matsalar manoma da makiyaya”.

Malamin na harkokin siyasa ya kuma fadi muhimmancin da hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma Kano wajen samarda aiki ga mutanen Kaduna.

“Akwai kauyuka da dama da ke kan wannan titin kuma akasarinsu noma da kiwo al’ummarsu ke yi, lalacewar hanyar ya shafi yadda suke fitar da abinci da kuma dabbobinsu domin sayarwa, mutane basu son bin hanyar saboda lalacewarta.

Idan aka kammala aikin hanyar manona za su yi farin ciki domin za su rika fitar da abinci da su ke nomawa zuwa wurare da dama cikin sauki” inji Dr. Tukur.

Inganta ilimi

Wani kalubale da ke gaban Sanata Uba Sani shi ne yiwa harkar ilimi garambawul a Kaduna.

Dr. Tukur ya ce a halin da ake ciki sakamakon jarrabawa na makarantun sakandare a Kaduna babu yabo babu fallasa ne kuma ya kamata a ce dalibai da ke karatu a makarantun jihar su ciri tuta.

Baya ga wannan ya ce akwai matsala a jami’o’i

“Jami’o’i na fuskantar kalubale, ya kamata a samar da litattafai da kayan aiki da inganta albashin ma’aikata da kuma saukakewa dalibai kudin makaranta” a cewar Dr. Tukur.

Masanin siyasar ya kuma yi kira ga sabuwar gwamnati ta farfado da kwalejojin koyar da aikin yi da ke jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here