Ali Nuhu ya zama jakadan kamfanin cingam

0
223

Jarumi, mashiryin fina-finai kuma darakta a masana’antar Kannywood, Ali Nuhu ya zama jakadan kamfanin kayayyakin abinci na Sumal Foods Limited.

Kamfanin dai ya dade yana samar wa ’yan Najeriya da ma makwabtan kasashe ingantattun kayayyakinsu da suka hada da biskit da alawa da cingam, tun sama da shekaru 40 da suka gabata.

Yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da jarumin, Janar Manajan kamfanin, V. P Sudarson, ya bayyana cewa sun yanke shawarar zabar Ali Nuhu ne ba don shuhurar da ya yi kawai ba, sai dai saboda ayyukan da yake yi na taimakon al’umma wanda mutane da yawa suke amfana da shi.

Sudarson ya kuma ba wa ’yan Najeriya tabbacin cewa kamfaninsu zai ci gaba da samar da kayayyakin abinci masu kara lafiya da saukin kudi kamar yadda ya saba.

Ya ce kamfanin na Sumal da Ali Nuhu za su yi amfani da wannan hadin gwiwa don samar wa al’ummar kasar kayayyakin masu kyau da kuma samar musu da damarmaki don bayar da tasu gudunmawar wajen ci gaban al’umma.

Yayin da yake jawabi a lokacin rattaba hannu kan takardar yarejeniyar, jarumi Ali Nuhu ya yi alkawarin daukaka kayayyakin kamfanin zuwa lunguna da sakunan fadin kasar nan.

“A matsayina na wanda ya hada gwiwa da wannan kamfanin, zan yi amfani da damata wajen kawo wa ’yan Najeriya abubuwan nishadi masu kyau da kuma ingantattun kayan abinci masu kara lafiya.

Jarumin ya kuma ba diloli da masu kasuwancin kayan kamfanin tabbacin bayar da gudunmawarsa wajen ci gaban kasuwancinsu a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here