Diezani ta maka EFCC a gaban kotu tana neman diyyar biliyan 100

0
116

Tsohuwar ministar Man Fetur, Diezani Alison-Madueke ta bukaci Hukumar Yaki da Rashawa ta EFCC da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya su biya ta diyyar Naira biliyan 100 saboda bata mata suna.

A cikin karar wacce lauyanta, Mike Ozekhome (SAN) ya shigar, Diezani ta kuma bukaci kotun ta tilasta wa EFCC ta wallafa mata sakon ban-hakuri a cikin akalla manyan jaridu guda uku.

Tsohuwar Ministar ta kuma ce dole jaridun su hada da Thisday da Punch da kuma The Sun, kuma a yi wallafar cikin kwana bakwai da yanke hukuncin kotun.

Ta ce wallafe-wallafen da EFCC ta yi a kanta, ta yi su ne da nufin bata mata suna da tozarta ta da cin zarafinta tare da mayar da ita abar dariya a idon duniya.

Ta ce takamaimai, ta shigar da karar ce a kan wasu sarkoki da kayan kwalliya da suka kai na Dalar Amurka miliyan 40, wadanda aka ce nata ne, saboda babu wata kwakkwarar hujja a kan haka, har zuwa lokacin da kotu ta ba da umarnin kwace su.

Ta kuma ce a karshen wa’adin mulkin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ta kamu da cutar sankarar mama, inda aka garzaya da ita Ingila don ganin likita a ranar 22 ga watan mayun 2015, kuma tun lokacin take ci gaba da samun kulawar likitoci a can.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here