Kenyatta ya bukaci Tinubu ya maida hankali wajen samar da hadin kan kasar

0
117

Tsohon shugaban Kenya Uhuru Kenyatta, ya bukaci shugaban kasar Najeriya mai jiran gado Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, ya yi kokarin wajen hada kan ‘yan kasar ba tare da nuna banbancin addini ko kabila ko kuma siyasa ba.

Kenyatta ya bayyana hakan ne a lokacin taron lakca da kwamitin mika mulki ya shirya a garin Abuja, gabanin rantsar da sabuwar gwamnatin Tinubu.

Tsohon shugaban na Kenya ya ce yayinda ake samun rarrabuwar kai a lokacin zabe, abinda ya fi kamata sabuwar gwamnati ta yi shine hada kan al’umma, lamarin da ya sa shi bukatar Tinubu ya lallashi duk wadanda aka sabawa don samar da ci gaba a kasar.

Shima da ya ke na shi jawabin, shugaba Muhammadu Buhari mai barin gado, ya ce tsarin dimukaradiya ba wai kawai tsarin gudanarwar gwamnati ba ne, tsari ne na gudanar da rayuwa, don haka ya ce akwai bukatar baiwa kowane dan kasa dama don cin gajiyar romon dimukaradiya.

Da ya ke maida jawabi, shugaban Najeriya mai jiran gado Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, wanda zababben mataimakin sa Sanata Kashim Shattima ya wakilta, ya yi kira ga ‘yan Najeriya su marawa sabuwar gwamnatin su baya, don samar da sabuwar Najeriya.

A ranar Litinin mai zuwa za’a rantsar da Tinubu a matsayin sabon shugaban kasar, bayan lashe zaben da aka yi a watan Fabarairun da ya gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here