‘Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane 26 a Nasarawa

0
82

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Nasarawa ta sanar da nasarar kama wasu mutane 26 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da ke addabar zaman mazauna jihar.

Rundunar ta kuma ce jami’anta sun ceto biyu daga cikin mutane da aka yi garkuwa da su kwanan nan daga karamar hukumar Wamba da ke jihar a samamen da suka kai.

Da yake gabatar da dukkan wadanda ake zargi da aikata laifuka da aka kama da laifuka daban-daban a fadin jihar, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya ce rundunar ta kama wasu mutane 13 da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne da suka addabi mazauna karamar hukumar Karu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here