Abba Gida-gida ya koka da yadda Ganduje ya bar masa bashi mai tarin yawa

0
91

Sabon Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya Koka da yadda tsohon gwamnan kano Abdullahi Umar Ganduje ya bar masa bashin da yakai sama da Naira Biliyan 241.5

”Wanann abun da tsohuwar gwamnati ta yi mana abun takaici ne, a Ina za mu samu wadannan kudaden har mu biya”. Inji Abba Kabir

Sabon gwamnan ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ya karɓi ragamar mulkin jihar Kano a gidan gwamnatin Kano.

Abba Kabir Yusuf ya bada tabbacin zai duba yadda gwamnatin tada gabata ta gudanar da mulkin da kuma daukar matakan da suka dace.

Sannan kuma ya baiwa al’ummar jihar Kano tabbacin gwamnatin sa zata yi duk mai yiyuwa wajen ganin bai basu kunya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here