A daina fargaba muna da wadataccen mai – NNPC

0
139

Yayin da aka fara dogayen layuka a gidajen mai a wasu sassa na Najeriya bayan sanarwar cire tallafin mai da sabon shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya ce zai yi, kamfanin mai na NNPC, ya ce jama’a su daina fargaba domin akwai wadataccen mai a kasa.

Shugaban kamfanin, Malam Mele Kyari, ya shaida wa BBC cewa, akwai mai don haka babu wata matsala da ya ke gani za a iya fuskanta data shafi karancin mai.

“Dama duk lokacin da aka samu irin wannan jawabi daga shugabanni, sai mutane su yi ta tururuwa suna zuwa gidajen mai suna siyan mai fiye da wanda suke bukata saboda suna tsoro kada a kara kudin man” a cewar Kyari.

Ya kara da cewa bai ga abin tsoro ba domin akwai mai sosai a kasa.

Dangane da batun cire tallafin man kuwa, shugaban na NNPC, ya ce dama tallafin ya jima da zame wa NNPC matsala, domin kudin kamfanin ake dauka ana biyan tallafin.

Ya ce, “Abin da shugaban kasar ya yi ya zo dai-dai da dokar kasa, domin matakin hakan ya dace sosai”.

Shi ma shugaban hukumar da ke kula da tsare-tsare da sa ido a kan harkokin man fetur a Najeriyar NMDPRA Malam Faruk Ahmed, ya ce za su tabbatar farashin man bai wuce kima ba.

Ya ce, “Matakin shugaban kasar ya yi dai-dai da doka, domin tun a bara ya kamata a cire tallafin man”.

Bayan rantsuwar kama aiki ne, sabon shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya sanar da cire tallafin man, yana cewa gwamnatinsa za ta karkata kuɗaɗen zuwa wasu ɓangarorin ci gaban ƙasa.

“Tallafin man fetur ya tafi,” in ji shi. “Muna yaba wa tsohuwar gwamnati bisa ƙoƙarin janye tallafin man fetur a hankali, wanda yake ƙara wa mai ƙarfi ƙarfi fiye da talaka.”

Ya ƙara da cewa: “Ba zai yiwu tallafin ya ci gaba da laƙume kuɗaɗe ba yayin da muke ƙarancin kuɗi.

A madadin haka, za mu mayar da kuɗin wajen ayyukan raya ƙasa, da ilimi, da harkokin lafiya, da kuma ayyukan da za su kyautata rayuwar miliyoyin ‘yan ƙasa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here