Kotu ta ba da umarnin kara kama dakta Idris Abdulaziz

0
110

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da keJihar Bauchi ta bayar da umarnin kamo Sheikh Idris Abdul’aziz dai

Malamin a kwanakin baya ya fito daga gidan yari bayan shafe sati guda da ya yi a tsare, kan zargin tada zaune tsaye da ke barazana ga zaman lafiyan jihar.

Yansanda ne suka fara gabatar da shi a kotun majistire, amma daga bisani ma’aikatar shari’a ta Jihar Bauchi ta amshi ragamar shari’ar.

Tun da farko dai kotun ta tura shi gidan yari amma daga baya aka sake shi.

Sai dai kuma bayan fitowarsa ne aka sake mayar da shari’ar da ake masa daga kotun majistiren zuwa kotun shari’ar Musulunci, inda aka shiga kotun a ranar Laraba.

A zaman da kotun da aka yi a ranar Laraba, alkalin kotun, Malam Hussaini Turaki, ya nuna rashin jin dadinsa bisa kasa amsa gayyatar da kotun ta yi wa Malamin domin amsa Shari’ar da ke gabansa.

Lauyoyin Malamin dai sun shaida wa kotun cewa, a daren jiya rashin lafiya ta riski Malamin, don haka ba zai iya samun damar halartar zaman kotun ba.

Da aka nemi su bayar da takardar tabbacin rashin lafiya daga wani alkali hakan bai samu ba.

Lauyan gwamnatin jihar masu shigar da kara ya bukaci kotun da ta bayar da umarnin kamo Malamin a duk inda aka yi tozali da shi.

Da yake yanke hukunci kan bukatar, alkali Malam Hussaini Turaki ya ce rashin amsa gayyatar tamkarar rashin daraja kotun ne.

Barista Aliyu Ibn Idris, Babban Lauyan gwamnatin Jihar Bauchi, ya shaida wa manema labarai cewa, wanda ake kara bai bayyana a kotun ba, amma ya shigar da bukatar cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar da ake masa ta bakin lauyoyinsa.

“Mu kuma muka yi jayayyar cewa dole ne ya fara bayyana a gaban kotun sai ya gabatar da bukatar cewa kotun ba ta da hurumin sauraron karar.

“Amma da yake bai zo kotun ba, mun gabatar da bukatar a cafko shi tun da ya ki zuwa gaban kotu. Kuma kotun ta amince da wannan bukatar ta mu. Don haka yanzu ko ta dage cikin da sauraron karar zuwa ranar Litinin domin cigaba da sauraro.”

Shi kuma Lauyan malamin, Sadik Abubakar Ilelah, ya ce, sun bukaci a bai wa malamin wata rana domin ya samu damar zuwa amma kotun ta ki amince da hakan, ya ce ba wai sun ki mutunta gayyatar kotun ba ne, illa wanda suke karewan baya da lafiya ne.

A cewarsa, “An sauyo shari’ar ne domin ambato daga kotun majistire zuwa kotun shari’ar musulunci, amma wanda muke karewa bai samu zuwa kotu ba domin rashin lafiyar da yake fama da ita, don haka ba zai zai samu halartar zaman kotun na yau ba. Mun roki a ba shi wani ranar da zai samu ya zo tun da yau ne a ranar farko da aka fara sauraron karar, amma sun ki amince da bukatar da cewa mun ki biyayya wa gayyatar kotu.

“Kotu bayan sauraron muhawarar kowani bangare ta bada umarnin a kamo shi domin ya bayyana bisa dole.”

Baristan ya ce za su yi tunanin daukan matakin da ya dace a bisa amfani da tsarin doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here