Messi zai fayyace makomarsa amma ba zai je Barcalona ba

0
261

Ana sa ran nan gaba kadan Lionel Messi zai fayyace kungiyar da zai koma taka leda a kakar badi – sai dai ba zai koma Barcelona ba in ji Guillem Balague.

Messi zai so sake komawa kungiyar da ya fara yi wa tamaula tun yana da shekara 12 da haihuwa, a lokacin da ya bar Argentina .

To sai dai wakilansa sun sanar da kungiyar ta Camp Nou cewar cikin gaggawa zai fayyace inda zai koma, ba za su jira kunshin kwantiragin da kungiyar ta Sifaniya za ta gabatar masa ba.

Messi, mai shekara 35, wanda ya lashe kofin duniya a Qatar a 2022 na son ci gaba da murza leda a Turai, amma dai ta tabbata cewar zai bar Paris St Germain, wanda yarjejeniyarsa za ta cika a karshen watan Yuli.

A Saudi Arabia, jami’an gwamnatin kasar na tsara yadda za su tarbi kyaftin din Argentina.

Ana cewa Messi ya amince da yarjejeniya mai dan karen tsoka da Al-Hilal ta yi masa tayi, domin ya koma can da murza leda.

Kenan wakilansa na shirye-shiryen sanar da hukuncin da zai yanke – ana cewa ita ce kwantiragi mafi daraja a duniya.

Kungiyar Amurka da ake kira Inter Miami tana cikin masu son daukar Messi, amma wasannin aro take fatan ya yi mata kaman yadda Barcelona ma take fatan ya buga mata wasannin aro.

Yanzu dai Messi ake jira ya yanke shawara kan kungiyar da zai buga wa tamaula nan gaba, sannan a sanar da duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here