Za mu yi fito-na-fito da gwamnati kan shirin cire tallafin man fetur – NLC

0
134

Kungiyar kwadagon Najeriya ta sha alwashin yin fito na fito da gwamnatin kasar a kan yunkurin da sabon shugaban Najeriyar ke yi na janye tallafin mai.

Kungiyar ta ce ba za ta amince ba, saboda janye tallafin zai jefa al’umma a cikin wahala.

Tun bayan sanarwar da shugaba Tinubu ya yi a ranar da aka rantsar da shi aka fara dogayen layukan mai a sassan kasar.

Kwamarade Nasir Kabir shi ne sakataren tsare-tsare na Kungiyar NLC ya shaida wa BBC cewa shugaban Najeriyar ya yi hanzarin sanar shirin cire tallafin man fetur ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ba.

Kafin ka janye tallafi sai ka kawo wutar lantarki, tituna duk sun wadata talakawa sun rabu da talauci a kasa, ake maganar gwamnati ba ta hannu a cikin wannan abu”, in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here