Home Labarai Kasuwanci An kara farashin litar man fetur zuwa naira 540 a Najeriya –...

An kara farashin litar man fetur zuwa naira 540 a Najeriya – NNPC

0
74

Kamfanin main a Najeriya, NNPC, ya tabbatar da karin farashin litar mai a fadin kasar.

Mai Magana da yawun kamfanin, Garba Deen Muhammad, shine ya tabbatar da hakan a awata ssanarwa da ya fitar.

‘Yan Najeriya sun tashi da labarin hauhawar farashin na man fetur daga naira 197 zuwa sama da naira 500.

A cewar rahotanni daga kasar, an fitar da jadawalin yadda za a sayar da farashin man fetur a shiyyoyin kasar.

Sanarwar da kamfanin NNPC ya fitar ta ce, dokar sabon farashin man, za ta fara aiki ne daga ranar 31 ga watan Mayun 2023.

A cewar sabon farashin, farashin man fetur a Maiduguri ya koma naira 557 kan kowacce lita, yayin da Damaturu, Yobe, da sauran jihohin Arewa maso Gabas, farashin ya tasamma naira 550 kan kowacce lita.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Birnin Kebbi da sauran jihohin Arewa maso Yamma, za su sayi man fetur akan naira 545.

Yankin jihohin Arewa ta Tsakiya, farashin man ya tsaya a kan naira 537 kan kowacce lita, sai dai banda Illorin, da nasu farashin litar man ya tsaya akan naira N515.

Sanarwar ta NNPC ta ce, Kudu maso Kudancin Najeriya za su sayi litar mai akan naira 520, sai dai banda Uyo da Yenegoa wanda farashin man ya tsaya akan naira 515 kan kowacce lita, inda sauran jihohin Kudu maso Kudu farashin su na litar mai ya tsaya akan naira N511.

A jawabin da ya gabatarwa al’ummar Najeriya ranar bikin rantsuwar kama aiki, sabon shugaban kasar, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar da cewa bakin alkalami ya riga ya bushe kan batun janye tallafin man fetur. Jim kadan bayan gabatar da wannan jawabin ne kuma, gidajen mai suka fara cika da ababen hawa, domin kaucewa tsadar man fetur din a sassan kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

X whatsapp