Faransa ta kaddamar da shirin koyar da harshen Faransanci a Najeriya

0
63

Faransa ta kaddamar da wani shirin bunkasa koyar da harshen Faransanci a makarantun Lagos dake kudancin Najeriya,  karkashin wata yarjejeniya da za’a sabunta tsakanin gwamnatin jihar da karamar ministan raya kasa da dangantaka tsakanin kasashe na Faransa Uwargida Chrysula Zacharopulu dake ziyara a Najeriya

Uwargida Chrysoula Zacharopoulou na ziyara a Najeriya ce, tun ranar 28 ga watan Mayu, inda ta halarci bukin ranstsar da sabon shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu kafin ta karasa birinin Lagos.

Uwargida Chrysoula Zacharopoulou yayin sanya hannu kan shirin.
Uwargida Chrysoula Zacharopoulou yayin sanya hannu kan shirin. © rfi/abba

Bikin sanya hannu kan yarjeniniyar, wata dama ce ta sake tabbatar da kawancen da akayi a baya da kuma kaddamar da sabon shirin koyar da harshen Faransaci a makarantun sakandaren gwamnati a zamanance.

Kafin bukin da zai gudana yau a birin Legas, sai da karamar ministan ta Faranasa dake kula da cigaban kasa da dangantar kasa-da-kasa da kuma raya harshen Faransanci ta kai ziyara birnin ilori na jihar kwara, inda suka sanya hannun kan yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatin jihar kan ayyukan gona da raya al’adu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here