Akalla mutane 28 ne suka mutu, sama da 300 kuma suka jikkata, kana ana fargabar da dama sun makale a wani hatsarin jirgin kasa da ya afku a jihar Odisha da ke gabashin Indiya.
Hukumomin kasar sun shaidawa kafafen yada labarai na cikin gida cewa jirgin fasinja na Coromandel Express da wani jirgin kaya sun yi karo a kusa da Balasore mai tazarar kilomita 200 daga Bhubaneswar babban birnin jihar.
Wani jirgin fasinja na biyu shi ma ya shiga cikin lamarin, a cewar babban sakatare na Odisha Pradeep Jena, amma har yanzu ba a fayyace yadda lamarin ya kasance ba.
Jaridar Trust ta Indiya ta ce, kimanin mutane 50 ne ake fargabar sun mutu, a cewar, kuma akwai fasinjoji da yawa da suka makale a karkashin jiragen.
Wani jami’in ‘dan sanda a Balasore ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa da yawa daga cikin wadanda suka jikkata na cikin wani mawuyacin hali, sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken bayani ba.
Kafofin yada labarai na cikin gida sun ce adadin fasinjojin da suka jikkata ya haura 300.
Firaministan Indiya Narendra Modi ya nuna damuwa ainun kan lamarin.