Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya musanta ikirarin da ake yi na cewa ya bayyana kadarorin da ya kai naira Tiriliyan 9.
Gwamnan ya musanta jita-jitar ce wadda ya bayyana a matsayin kanzon kurege a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Idris ya fitar a ranar Juma’a a Gusau.
Dare ya bayyana labarin a matsayin kage da aka shirya domin kawar da hankalin sabuwar gwamnati daga yunkurinta na ceto Zamfara.
Ya kara da cewa wadanda suka fadi zabe ne suka yada karairayin, kamar yadda suka yi a lokacin yakin neman zabe.
Sanarwar ta bayyana cewa sabuwar gwamnati ta fara aiki kuma ta mayar da hankali wajen ganin ta samar da nutsuwar da ake bukata a cikin harkokin mulki a jihar domin sauke nauyin alhakin da ke kan ta.
Sanarwar ta kara da cewa: “Ba za a dauke mana hankali da irin wadannan labaran na karya da ke kafafen sada zumunta ba, domin gwamnatinmu ta kuduri aniya kuma ta mayar da hankali kan kudirinta na magance matsalar tsaro da ilimi da samar da ruwan sha da inganta kiwon lafiya da noma da sauran kalubalen tattalin arziki da suka addabi jihar.
“Muna kuma aiki ba dare ba rana domin ganin mun sauke nauyi da ayyukan da gwamna ya yi alkawrin gudanarwa,” kamar yadda sanarwar ta ce.
Gwamnan ta bakin mai magana da yawunsa ya ce gwamnatinsa na matukar aiki a kokarinta na cetowa da kuma sake gina Jihar Zamfara, inda ta mayar da hankali wajen ganin ta cika alkawuranta.
Ya kuma bukaci jama’a da su yi watsi da karyar da ake yadawa da gangan domin a bata wa sabuwar gwamnatinsa suna.