Shawarwarin tsohon shugaban kasa Babangida ga Tinubu

0
142

Tsohon Shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya bukaci zababben Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya yi amfani da kwarewarsa wajen magance kalubalen tattalin arzikin da Nijeriya ke fuskanta cikin gaggawa.

Babangida ya bayyana haka ne a ranar Litinin a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise TB, inda ya kuma taya Shugaban kasa, Tinubu da mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima murna rantsar da su da aka yi.

Haka kuma IBB ya bayyana Tinubu a matsayin hazikin dan siyasa, yayin da ya bukace shi da ya sake fasalin rundunar sojojin Nijeriya da kuma zaburar da manyan masu karfin tattalin arzikin kasar nan wajen zuwa jari.

“Tinubu kwararren dan siyasa ne wanda ke bukatar yin amfani da basirarsa wajen hada kan al’ummar da ke fama da rikici.
“Dole ne ya zaburar da manyan masu karfin tattalin arzikin Nijeriya na gida da waje, domin magance matsalar tattalin arzikin kasa nan tare da sake fasalin rundunar soji.
“A matsayinsa na babban kwamandan rundunar sojin Nijeriya, akwai bukatar ya sake fasalin rundunonin tsaro ta yadda za a sake farfado da su, da horar da su da kuma sake tsara su yadda ya kamata, saboda akwai babban jan aiki a gaban rundunonin tsaro wajen hada kansu da inganta su,” in ji Babangida.

Babangida ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya su yi hakuri da sabuwar gwamnatin Tinubu.
Ya jaddada cewa, Tinubu na bukatar samun damar hada kan Nijeriya, yana mai bayyana ra’ayin cewa akwai mutane masu basira da za su iya taimaka masa wajen gyara kowane fanni ciki har da sojojin kasar nan.

Babangida ya yi kira ga Tinubu ya zama shugaban kasa ga dukkan ‘yan Nijeriya a daidai lokacin da ya karbi ragamar shugabancin kasar nan.

“Ina yi wa sabuwar gwamnati fatan alheri. Su sanya Nijeriya a gabansu da kuma jin dadin ‘yan Nijeriya, ya kamata wannan ya zama mafi muhimmanci. Shugabanci ya tabarbare a dukkan matakai da ke kasar nan.

“Shawarar kawai ita ce su yi hakuri kuma su ci gaba da tallafa wa sabuwar gwamnati, amma idan sun ga abubuwa suna faruwa ba daidai ba, su yi kokarin yin kira kamar yadda suka saba, amma su kasance masu hakuri game da shugabanci,” in ji Babangida.

Babban jojin Nijeriya, Olukayode Ariwoola ne ya rantsar da Tinubu da Shettima a matsayin shugaban kasa da mataimakinsa.

Mai shari’a Ariwoola ya rantsar da Tinubu da Shettima ne a dandalin Eagles Skuare da ke babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here