Tinubu ya ba da umarnin bai wa ’yan Najeriya tallafi

0
158

Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) Mele Kyari ne ya sanar da haka, yana mai cewa biyan tallafin mai da gwamnati ke yi ya zama tarihi, hasali ma ba a ware masa ko sisi ba a kasafin kudi.

Da yake bayani bayan ganawarsa da jagororin jam’iyyar APC mai mulki, Kyari ya ce a halin yanzu ma NNPC na bin gwamnati bashin Naira tiriliyan 2.8 da ya kashe wajen biyan tallafin man, don haka kamfanin ba zai iya ci gaba da biya ba.

“Har yanzu gwamnati ta kasa biyan Naira 2.8 da muke bin ta, wanda ya isa hujja cewa gwamnati ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin man ba,” in ji Kyari.

Ya bayyana cewa babu wanda zai ba da bashi ga wanda ake bi bashin Naira tiriliyyan 2.8, don haka, kamfanin NNPCL ba zai iya kara biyan tallafin a madadin gwamnati ba.

Hasali ma kudin da NNPC ke kashewa wajen biyan tallafin na hana shi sauke nauyin da ya rataya a kansa, ga shi kasa na bukatar kudaden aiwatar da manyan ayyuka da samar da ababen more rayuwa.

A gefe guda kuma, kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dauki matakan da za su hana cire tallafin man jefa ’yan kasar cikin karin matsin rayuwa.

Mukaddashin daraktan Amnesty International, Isa Sanusi, ya shawarci gwamnati ta yi hattara kada matakin nata ya kara talauta ’yan kasar “wadanda da kyar suke iya biyan kudin makaranta da na asibiti da kuma cefani.

“Ga shi kuma har yanzu gwamnatin ba ta fayyyace matakan da za ta dauka domin rage radadin cire tallafin a kan masu karamin karfi ba.

“Bai kamata cire tallafin ya kara kawo kuncin rayuwa ga jama’a ba, don haka akwai bukatar daukar matakai da za su samar da sauki bayan janye tallafin man.

“Bai dace Najeriya ta ci gaba da biyan tallafin da aka dade ana wuru-wuru da shi ba, kuma ya kamata gwamnati ta amsa kiraye-kirayen hukunta duk wadanda aka samu da laifi a badakalar tallafin mai a rahoton da majalisar dokoki ta gudanar — komai matsayin wanda aka kama da laifin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here