Yadda aka kammala gasar Firimiya ta bana

0
85

Tuni aka kammala gasar Premier League ta kakar wasa ta 2022 zuwa 2023, wadda Manchester City ta lashe kofin bana bayan da aka fara bikin bude makon farko ranar 5 ga watan Agustan 2022, sannan aka kammala ranar 28 ga watan Mayun 2023.

An yi wasanni 380 da cin kwallo 1,084 daga ciki Erling Haarling ya zura 36 a raga, ba wanda ke gabansa a wannan bajintar a kakar wasansa ta farko daya buga a Manches-ter City.

Kungiyar ta da lashe Premier League:
Manchester City ce ta dauki kofin bana da maki 89, wadda ta lashe na uku a jere na biyar a kaka shida, amma na bakwai jimilla bayan ta doke Arsenal wadda ta kwashe kwanaki 248 tana jan ragama.

Kungiyoyin ukun da suka bar Premier League:
Leicester City, Leeds United, Southampton
Wadanda za su buga Champions League a badi:
Manchester City, Arsenal, Manchester United, Newcastle United
Wadanda za su wakilci Ingila a Europa League:
Liberpool, Brighton & Hobe Albion, Wadda za ta wakilci Ingila a Europa Conference League. Aston Villa
Fitatcen mai tsaron raga:
Dabid de Gea na Manchester United, (Wasa 17 kwallo bai shiga ragarsa ba)
Wasan da kungiyar gida ta ci kwallaye da yawa:Liverpool  9–0 Bournemouth, (Ranar 27 ga watan Agustan 2022), Karawar da aka ci kungiyar da ke gida kwallaye da yawa: Leeds United 1–6 Liverpool
(Ranar 17 ga watan Afirilun 2023) Wasannin da aka zura kwallaye da yawa a raga:
Liverpool 9–0 Bournemouth (Ranar 27 ga watan Agustan 2022) Manchester City 6–3 Manchester United (Ranar 2 ga watan Oktoban 2022) Kungiyar da ta jere cin wasanni:
Manchester City karawa 12 Wadda ta yi wasa da yawa ba tare da an doke ta ba:
Newcastle United fafatawa 17 Kungiyar da ta yi karawa da yawa ba tare da yin nasara ba:
Southampton wasa 13 Wadda ta yi rashin nasara da yawa a jere: Leicester City wadda aka ci fafatawa shida a jere Southampton wadda aka doke karo shida a jere -a jere

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here