Mutanen da wani hatsarin jirgin kasa ya kashe a India sun kai 288

0
111

Akalla mutane 288 ne suka mutu yayin da fiye da 850 suka jikkata a wani mummunan hatsarin jirgin kasa da ya afku a kasar Indiya, a wani hatsarin jirgin kasa mafi muni da kasar ta gani cikin sama da shekaru 20.

Har ya zuwa wayewan garin Asabar masu aikin ceto da kokarin gano masu sauran nunfashi karkashin karagun jiragen kasa guda ukun da suka kife sakamakon hatsarin na yammacin Juma’a.

Hotunan wurin da hatsarin ya afku sun nuna tarkacen karagun jiragen da kuma yadda jinni ke malala a yankin Balasore, na jihar Odisha da ke gabashin India.

Hatsari mafi muni

Hadduran jiragen kasa dai ba sabon abu bane a kasar Indiya, mafi muni da kasar ta gani shine a shekarar 1981, lokacin da wani jirgin kasa ya kauce hanya tsallaka wata gada a Bihar ya fada cikin kogin, inda nan take mutane tsakanin 800 zuwa 1,000 suka mutu.

Jiragen kasan da suka yi hadari a yankin Odisha dake Gabashin  Índia. 02/06/23.
Jiragen kasan da suka yi hadari a yankin Odisha dake Gabashin Índia. 02/06/23. REUTERS – STRINGER

To sai an yi imanin cewa hadarin na ranar Juma’a shi ne mafi muni tun daga shekarun 1990.

Babban sakatare na jihar Odisha Pradeep Jena ya tabbatar da cewa, kimanin mutane 850 ne suka jikkata kuma sun kwance a asibitoci sakamakon hadarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here