‘Yan sanda sun rufe majalisar dokokin Nasarawa kan rikicin shugabanci

0
81

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta rufe harabar majalisar dokokin jihar, domin kaucewa tabarbarewar doka da oda biyo bayan samun shugabanni biyu na majalisar wakilan ta bakwai.

DSP Ramhan Nansel, kakakin rundunar ‘yansandan jihar, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a cikin wata sanarwa a garin Lafia.

Nansel ya ce an dauki matakin ne saboda umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar Mista Maiyaki Mohammed-Baba.

Ya ce kwamishinan ya bada umarnin ne bayan tattaunawa da sauran hukumomin tsaro a jihar.

Kamfanin dillancin labarai (NAN) ya tattaro cewa zababbun mambobin majalisar a ranar Talata, 6 ga watan Yuni sun gudanar da ayyuka guda biyu masu kama da juna wanda ya haifar da fitar da shugabannin majalisar guda biyu daban-daban.

An girke jami’an tsaro a harabar majalisar da sanyin safiyar ranar Laraba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here