Abin da ya sa hare-haren ‘yan bindiga suka sake kunno kai a Nijeriya

0
86

Tun bayan rantsar da sabuwar gwamnatin shugaba Bola Tinubu da wasu sabbin gwamnonin jihohi a karshen watan jiya a Nijeriya, ‘yan kasar da dama suka rika fatan kyautatuwar al’amura musamman ta fuskar tsaro.

Babban kalubalen da tsohuwar gwamnatin da ya gada ta fuskanta shi ne matsalar tsaro, ko da yake ‘yan watanni kafin karshen wa’adin mulkin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari hare-haren ‘yan bindiga da satar mutane, wadanda arewacin kasar ke fama da su, sun dan lafa.

Sai dai a kasa da mako biyu bayan fara mulkin sabuwar gwamnatin kasar da wasu gwamnonin jihohi, hare-haren sun sake kunno kai, lamarin da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 80 jimulla.

Misali, a karshen makon jiya a jihar Sokoto, wasu mahara sun kashe fiye da mutum 50 a kananan hukumomin Gwadabawa da Tangaza, a cewar ganau da kuma hukumomi.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, ASP Ahmad Rufai, ya fitar ta ce ‘yan bindiga sun kai harin ne a kauyukan Raka, Bilingawa, Raka Dutse, Jaba, Dabagi da Tsalewa.

Haka zalika an kai wani hari da shi ma ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutum 30 a kauyukan Janbako da Sakida da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara shi ma kuma a karshen makon jiya aka kai shi.

‘Yan bindigar sun kuma sace ‘yan mata sama da 30 da suka je yin itace a kauyen Gora ko da yake daga bisani wasu daga cikinsu su auna arziki sun koma gida.

A ranar Laraba a Yankin Babban Birnin Tarayyar kasar Abuja, wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Yangoji da ke karamar hukumar Kwaji.

Wani mazaunin kauyen mai suna Suleiman Musa ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN) cewa maharan sun kai harin ne a safiyar ranar Laraba, inda suka sace yarinya ‘yar shekara bakwai.

Ya ce maharan sun dirar wa kauyen ne inda suka yi harbe-harbe kafin suka fara shiga gidajen jama’a, kamar yadda ya ce, daukin da jami’an tsaro suka kawo ne ya sa maharan suka tsere.

A jihar Kaduna ma labarin haka yake, inda a farkon makon nan a karamar hukumar Birnin Gwari wasu mahara suka kashe wasu manoma biyu suka kuma suka sace mutane da dama.

A jihar Binuwai da ke tsakiyar kasar, ‘yan bindiga sun kashe akalla mutum 25 sannan suka cinna wa gidajensu wuta a harin da suka kai a karshen makon jiya a kauyen Imande Mbakange, a cewar wasu ganau.

Masani kan harkokin tsaro a Nijeriya Group Captain Sadiq Garba Shehu (mai ritaya) ya ce yana ganin dalilai biyu ne suka sa ake ganin kamar matsalar tsaro ta lafa a watannin baya.

“Ni ina ganin lafawar hare-haren kawai ta zo ne, amma ba wai an ci karfin masu kai hare-hare ba ne ko kuma sun daina yi ba. Da ma matsalar ba ta kare ba,” in ji shi.

Ya ce dalili na biyu shi ne “yawancin masu yin wannan hare-hare matasa ne majiya karfi. Tana yiwuwa lokacin da ake harkokin zabe hada-hadar zabe da kamfe da kudi da ake rarrabawa na zabe su suka dauki hankalinsu.

Suka je su ci kasuwar siyasa tukuna, bayan kuma an ci zabe an gama ‘yan siyasa sun tsuke bakin aljihunsu. To sai su sake koma wa kai hare-haren,” in ji shi.

Masanin ya ce har yanzu kasar ba ta yi nasarar magance matsalar hare-haren ‘yan bindiga ba da kuma satar mutane ba.

Ya ce gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ta karya lagon Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar, amma ba ta yi nasara kan matsalar hare- haren ‘yan bindiga da satar mutane a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiyar kasar ba.

“Wannan ya sa akwai jan aiki a gaban sabon Shugaba Tinubu wajen magance wannan matsalar,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here