Folashodun Adebisi: Wane ne gwamnan CBN na rikon kwarya?

0
163

An haifi Mista Folashodun Adebisi ranar 7 ga watan Maris na 1962.

A Juma’ar da ta gabata ce Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Folashodun Adebisi Shonubi a matsayin shugaban riko na Babban Bankin Najeriya CBN.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin Sakataren Gwamnati, Sanata George Akume, ta ce Mista Adebisi, wanda shi ne Mataimakin Gwamnan Babban Bankin, ya maye gurbin shugaban Babban Bankin, Godwin Emefiele wanda aka dakatar ‘nan take’.

 

An dakatar da Mista Emefiele ne bayan an gudanar da bincike a kan ofishinsa da kuma yadda ya tafiyar da sauye-sauye a fannin tattalin arziki.

“An umarci Mr Emefiele da ya yi gaggawar mika harkokin ofishinsa ga Mataimakin Gwamna (Bangaren Gudanarwa), wanda zai yi aiki a matsayin Gwamnan Banki na rikon kwarya kafin a kammala bincike da sauye-sauye,” in ji sanarwar.

Adebisi shi ne mataimakin shugaban CBN a bangaren gudanarwa tun daga watan Oktoba na 2018.

An haifi Mista Folashodun Adebisi ranar 7 ga watan Maris na 1962, kuma ya yi digirinsa na farko a fannin Injiniya a Jami’ar Legas daga 1978 zuwa 1983.

Kazalika ya yi digirinsa na biyu a Jami’ar ta Legas a fannin Injiniya a 1985. Kana daga bisani ya sake yin digiri na biyu a fannin harkokin kudi da kasuwanci daga 1988-1989.

Sabon shugaban CBN ya soma aiki a matsayin injiniya a kamfanin Mek-ind Associates daga 1984 zuwa 1989.

Daga 1989 zuwa 1990, ya zama babban jami’in kasuwanci na kamfanin Inlaks Computers Limited.

A shekarar ta 1990 ya samu aiki a bankin Citibank Nigeria Limited ko da yake ya bar bankin a 1993.

Daga nan Mista Adebisi ya yi aiki a wurare daban-daban da suka hada da Agusto & Co. Ltd da MBC International Limited.

Kazalika, ya yi aiki a First City Monument Bank (FCMB) daga 1999 zuwa 2002, da Ecobank Nigeria Plc daga 2003 zuwa 2007 inda ya kama aiki a kamfanin Renaissance Securities Nigeria Limited.

Sabon shugaban rikon na babban bankin Najeriya ya yi aiki a Union Bank of Nigeria Limited daga watan Satumba na 2009 zuwa Afrilun 2012.

Ya zama Manajan Daraktan Nigeria Inter-Bank Settlement System Plc daga watan Mayun 2012 zuwa Oktoban 2018.

Daga watan na Oktoban 2018, an nada Mista Folashodun a matsayin mataimakin shugaban babban bankin Najeriya (bangaren gudanarwa) kuma yana wakiltar shugaban babban bankin a Hukumar Tattara Haraji wato FIRS, tun daga watan Disambar 2019.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here