Cire tallafin mai: Ina jajanta mu ku, sadaukarwar ku ba za ta tafi a banza ba – Tinubu ga ‘yan Najeriya

0
148

A ranar Litinin ne shugaban kasa Bola Tinubu ya sake jajanta wa ‘yan Nijeriya kan radadin da suke ciki na janye tallafin man fetur a kwanakin baya.

A jawabinsa na ranar dimokuradiya ta 2023 a ranar 12 ga watan Yuni, shugaban kasar ya ce matakin da ya dauka na janye tallafin man fetur a lokacin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023, yayi ne don ceto kasar Nijeriya daga shiga hali mawuyaci ta yadda wasu ‘yan tsiraru marasa kishin kasa ke kwashe albarkatun kasar.

Ya roki ‘yan Nijeriya da su kara sadaukarwa kadan domin ci gaban kasar.

Ranar 12 ga watan Yuni ta kowacce shekara ce ake gudanar da bikin ranar dimokuradiyya domin karrama wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin 1993, Marigayi Cif Moshood Kashimawo Olawale (MKO) Abiola da sauran jaruman da suka sadaukar da rayuwarsu kan tabbatar da dimokuradiyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here