Rahotanni daga Jihar Kano sun bayyana cewar wani gini ya danne wasu mutane da ba a bayyana adadinsu ba a wajen dibar ‘ganima’ a ginin otal din Daula da gwamnatin Jihar ta rushe a baya-bayan nan.
Tuni dai hukumomin da ke alhakin kai dauki suka isa wurin da lamarin ya faru don ceto wadanda abun ya rutsa da su.