Tinubu ya yi ganawar sirri da Sanusi a fadar shugaban kasa

0
98

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri da Sarkin Kano na 14 kuma tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi, a fadar gwamnati.

Ziyarar ta Sanusi, wadda ita ce ta farko tun bayan da shugaban kasar ya hau kan karagar mulki, na zuwa ne mako guda bayan da shugaban kasar ya dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan CBN.

Kawo yanzu dai ba a fayyace abin da suka tattauna a ganawar tasu ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here