Kotu ta umarci DSS ta bai wa Emefiele damar ganin lauyansa fa iyalinsa

0
114

Wata babbar kotu a Abuja ta umarci daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Yusuf Bichi, da ya bai wa dakataccen gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele damar ganin lauyoyinsa da iyalinsa.

Kotun da ke zamanta a gundumar Maitama karkashin jagorancin mai shari’a Hamza Muazu, ta jaddada cewa bai Emefiele damar ma cikin hakkinsa da kundin tsarin mulki ya ba shi.

Umrnin kotun ya biyo bayan bukatar da lauyan Emefiele, J.B. Daudu, SAN, ya shigar, inda ya bayyana cewa DSS ta kasa amsa wasikun da aka rubuta a baya na neman samun damar ganawa da wanda yake karewa, mai kwanan wata 14 ga watan Yuni, 2023.

Lauyan Emefiele ya bayyana cewa ba a san DSS ta yi watsi da bukatunsu a baya sannan ta hana su gana wa da Emefiele.

Sai dai Awo ya bayyana kwarin gwiwar cewa hukumar tsaron za ta bi umarnin kotu tare da bai wa lauyoyin da aka lissafa da kuma iyalinsa damar ziyartarsa.

A halin da ake ciki dai, lauyoyin hukumar DSS da kuma ofishin babban mai shari’a na tarayya sun bukaci a tsawaita lokacin gabatar da martanin da suka bayar.

Kotun ta amince da bukatar, wanda ya kai ga dage sauraren karar zuwa ranar Talata, 19 ga watan Yuni, 2023, lokacin da za a ci gaba da sauraren karar.

Shugaba Tinubu ya dakatar da Emefiele, kafin daga bisani DSS ta yi awon gaba da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here