Sojojin Rasha nawa aka kashe a yaƙin Ukraine?

0
142

Rasha tana da tarihin sirri na ban mamaki game da asarar da ta yi a lokacin yaki. Don haka lokacin da ta mamaye Ukraine, BBC da abokan aikinta sun fara kokarin tantancewa da kuma kirga adadin wadanda suka mutu.

Jerin sunayen da aka tabbatar sun mutu – mutanen da muka san sun mutu – ya kai sama da mutane 25,000 da aka san sunayensu , wanda ya sanya mafi karancin asarar da Rasha ta yi.

Kididdigar ta bayar da kwakkwarar shaida kan yadda yakin ya shafi sojojin Rasha. Amma har ila yau ya bayar da amsoshi ga iyalai da ke fama da bakin cikin rashi.

Da yawan mutane ma ba su san abin da ya faru da ‘yan uwansu ba sai da BBC ta gano su.

Labarin sabbin ma’aikata biyu

Sgt Nikita Loburets, shugaban tawagar sojojin Rasha na musamman, ya mutu a ranar 20 ga Mayun bara a wani kauye da ke gabashin Ukraine. Shekarunsa 21 da haihuwa.

Kusan shekara daya bayan haka, dangin Alexander Zubkov sun sami labarin mutuwarsa a lokacin yakin Bakhmut. Yana da shekaru 34 kuma yana gidan yari an daure shi na shekaru tara saboda laifukan safaran miyagun kwayoyi, ya shiga kungiyar sojojin haya ta Wagner, wacce ke yaki a madadin Rasha, da fatan kubutar da kansa.

Wadannan biyu ne kawai daga cikin matattun mayaka 25,000 da BBC, da kafar yada labarai mai zaman kanta ta Mediazona ta Rasha, da kungiyar wasu ‘yan sa-kai ta bayyana, ta hanyar amfani da bayanai daga rahotannin hukuma, da jaridu, da kafofin sada zumunta, da sabbin kaburbura.

A tare, wadannan mutane biyu na nuni ga sauyin yanayin rundunar sojojin kasar Rasha tun bayan da suka mamaye kasar Ukraine – rundunar yakin da ke da dakaru wadanda shekarunsu suka ja, kuma me fama da matsalar rashin horo yayin da ake samun karuwar mace-mace.

Lokacin da aka fara yakin, misali, mayakin Rasha da aka tabbatar da mutuwarsa a kidayar BBC yana da kimanin shekaru 21 da haihuwa kuma mai karamin matsayi ne – kamar Sgt Nikita Loburets.

A cewar mahaifinsa Konstantin, Loburets ya so ya zama sojan sama tun kafin ya bar makaranta a Bryansk, wani birni mai nisan kilomita 100 daga kan iyaka da Ukraine. Ya fara karantar fasahar yaki kuma ya koyi yadda ake amfani da lemar sojoji-wato parachute, kafin kammala karatunsa.

A karshe, ya samu gurbin karatu a makarantar sakandare ta Ryazan Higher Airborne, makarantar horar da sojojin saman Rasha, kafin ya sami shiga rundunar soji ta musamman ta GRU, sashen leken asiri na rudunar sojin Rasha.

Kusan watanni uku da fara yakin, an afka wa Sgt Loburets da wani karamin rukunin sojin Rashawa a wani kauye da ke arewacin Kharkiv inda aka kashe shi, in ji mahaifinsa.

An binne shi a makabartar “Alley of Heroes” a garinsa kuma an ba shi lambar girma ta ‘Order of Courage’ bayan mutuwarsa.

Akwai dubban labarai irin nasa a cikin watannin farkon yakin.

Amma, yawansu ya ragu bayan shekara daya.

A cikin ‘yan watannin nan, misalin sojan Rasha da aka kashe a Ukraine, zai kasance wani mai shekaru 34 da aka dauka daga gidan yari.

A shekarar 2014, bayanan kotu sun nuna cewa ba shi da aikin yi, yana kuma da da daya a lokacin da aka same shi da laifin kisa kuma aka yanke masa hukuncin daurin shekaru takwas da watanni shida a gidan yari.

An yi masa afuwa aka sake shi a shekarar 2020. An sake gurfanar da shi a gaban kotu bisa tuhumarsa da laifin shan kwayoyi bayan shekara daya – bayan da aka kama shi da wani abokin tarayyansa suna dauke da 600g na haramtacciyar kwaya mai suna a-PVP.

Kotu ta sake yanke masa hukuncin daurin shekara tara, bayan ta yi la’akari da cewa ya rabu da matarsa kuma yana da karamin yaro da kuma wata ’yar’uwa da ke da nakasa wadda ya ke taimakawa wajen kula da ita.

Lokacin da kungiyar Wagner ta fara daukar ma’aikata daga gidajen yari, sai Zubkov ya shiga cikin watan Nuwambar bara bayan an yi masa alkawarin rubles 100,000 ($ 1,250; £ 1,000) kowanne wata. Idan ya gama hidimar wata shida, yana iya tsammanin za a ’yantar da shi.

Amma Zubkov ya mutu bayan watanni biyar, a lokacin da Wagner ta yi artabun kwace birnin Bakhmut na gabashin Ukraine – fadan da ya fi kowanne muni a yakin kawo yanzu. An binne shi a garinsu a ranar 28 ga watan Afrilu.

‘Karar da dakaru’

Ana amfani da Zubkov da sauran mutane ire-irensa a matsayin dakarun wucin-gadi in ji Dokta Jack Watling, kwararre kan yakin kasa a cibiyar tsaro ta Royal United Services Institute (Rusi)

Kididdidgarmu ta gano cewa fursunonin da ke gurfana a gaban kotu sun kama daga kananan barayi zuwa manyan masu laifi. A wani labari, wani mutum ya mutu a filin daga bayan an taba daure shi saboda kashe wani tsohon soja mai shekaru 92.

Tare da fararen hula da aka tara, wadanda aka dauko wasu daga kan titi ko kuma a kantunan kasuwa, ana ba su umarnin su rika gwabzawa da sojojin Ukraine a kullum, domin su sa su jikkata su tare da fallasa matsugunan su ga masu manyan makamai.

”Suna tura su gaba da sa ran cewa za a kashe su” a cewar Dokta Watlin.”Shi ya sa sojojin Rasha ke karewa da sauri”

Wannan canjin dabarun ya tabbata a kidayaar.

Rasaha ta yi asarar kwararrun dakaru masu yawa cikin watanni ukun farko na yakin.

Amma cikin watanni ukun baya baya nan, sojojin da ba su kware ba sun fi mutuwa.

Dokta Watling ya ce da gangan Rasha tana bayar da kariya ga sauran kwararrunta, tare da yin amfani da su wajen dakile hare-haren sari-ka-noke, sai dai kawai ta kai hare-hare da ba kasafai ba idan yanayi ya dace.

Kwararru na da wahalar samu yanzu. BBC ta tabbatar da mutuwar hafsoshin sojin Rasha sama da 2,100 – watakila saboda Rasha ta fi dogaro da kananan hafsoshi wajen jagorantar yaki fiye da kasashen yammacin duniya, lamarin da ke jefa su cikin hadari. Akalla 242 ne ke rike da mukamin Laftanar-Kanar ko sama da haka.

Kidayar mu ta nuna cewa an kashe matukan jiragen yaki akalla 159. Ba za a iya maye gurbin wadannan a kankanin lokaci ba: yana daukar akalla shekaru bakwai da miliyoyin daloli don horar da su.

Wannan asarar da aka yi ta tilasta wa tsoffin sojoji da suka yi murabus dawowa aiki, irin su Manjo Janar Kanamat Botashev.

A shekarar 2012 ne aka dakatar da aikinsa na soja a lokacin da ya ari wani jirgin yaki samfurin Su-27 ba tare da izini ba kuma ya fado da shi. A watan Mayun shekarar da ta gabata, yana da shekaru 63 a duniya, yana tuka jirgin Su-25 ne a lokacin da aka harbo shi a Luhansk da ke gabashin Ukraine.

Ba shi ne mutum mafi tsufa a cikin adadin matattu ba. Mikhail Shuvalov, ma’aikacin tashar wutar lantarki mai ritaya, ya yi aikinsa yana da shekaru 71. Kafofin yada labarai sun ce da farko an ki amincewa da shi, amma daga bisani ya je fagen daga aka kashe shi a ranar 10 ga Disamba.

Amintaccen bayani

An fara wannan kidayar ne saboda ma’aikatan BBC na Rasha sun san cewa in ba haka ba ba za a taba samun ingantaccen bayanan mace-mace ba.

Kowane bangare a cikin yakin yana rage asararsa. Sai dai Rasha tana da tarihin rufe adadin dakarunta da suka mutu a lokacin yakin fiye da abin da ya wajaba na sirrin soji ko kuma kishin kasar.

Shekaru da dama bayan karewar yakin Afganistan da na Checheniya, tsoffin sojoji da ‘yan uwa na ci gaba da fafutukar samun cikakkun bayanan mutanen da suka mutu.

Har yanzu ba a san tabbatacen adadin mutanen da suka mutu a yakin duniya na biyu ba.

Yin aiki tare da Mediazona da kuma bayanan da aka samu daga al’ummar Rasha, BBC ta tattara tare da tabbatar da mutuwar da jami’an hukumomin yankin suka ambata, ko a cikin rahotannin kafofin yada labarai ko daga iyalan wadanda abin ya shafa akan kafafen sada zumunta.

Sun sanya ido a wuraren tunawa da mayaka a fadin kasar don samun sabbin sunaye, kuma masu aikin sa kai sun dauki hotunan sabbin kaburbura, suna sanya suna da kuma asalin kowane mutum da aka tabbatar da mutuwarsa.

An gano sabbin makabartun mayakan Wagner, – shida a Rasha da daya a Luhansk a gabashin Ukraine – yayin da ake gudanar da kidayar. Daya, a Bakinskaya a kudancin Rasha, ana iya gani a hotunan tauraron dan adam yana kara habaka da sauri cikin watanni da yawa.

Adadin wadanda suka mutu a hukumance na baya-bayan nan a Rasha ya kai 5,937, a watan Satumban bara.

Amma adadin BBC ya riga ya kai fiye da 6,600 da aka tabbatar sun mutu a lokacin, kuma yanzu ya kai sama da 25,000.

A watan Fabrairu, jami’an leken asirin Birtaniya sun kiyasta cewa an kashe sojoji 40,000 zuwa 60,000.

Ma’aikatar tsaron Ukraine ta yi kiyasin cewa akwai sama da mutanen Rasha 200,000 da suka mutu – amma kuma wannan ya hada da wadanda suka jikkata.

Duk wadannan alkalumman sun shafe ikirarin Rasha na mutane 6,000.

BBC ta tuntubi gwamnatin Rasha don jin ta bakinta, amma ba ta mayar da wani martani ba.

Ba duk ‘yan Rashan da suka mutu ba ne aka kirga a kidayar mu ba -mun zakulo ne daga mutanen da aka ambata a majiyoyi daban-daban, ko a wuraren tunawa da mayaka da kuma a kan kaburbura da masu aikin sa kai suka ziyarta. Amma masu aikin sa kai ba za su iya karade duk fadin Rasha ba. Kuma kidayar ba ta hada da ‘yan aware masu magana da harshen Rashanci a Donbas ba.

Sai dai duk da cewa ba ta cika ba, kidayar tamu ta samu damar bayar da amsoshi ga wasu ‘yan uwar wadanda suka mutu, inda jami’ai suka kasa.

Labarin Anna

A lokacin da BBC ta tuntubi Anna-ba salin sunanta ba ne- a watan Disamba, kawai tana da zato game da abin da ya faru da Fail Nabiev, tsohon abokin zamanta kuma mahaifin ‘yarta.

An gano kabarin Nabiev a Bakinskaya, makabartar da aka gani daga hotunan tauraron dan’adam, kuma BBC ta gano sunansa.

Ya mutu a ranar 6 ga watan Oktoban bara, ya na da shekaru 60 da haihuwa, a awani fadan da ya kaure a kusa da Bakhmut-inda duka dakarun Wagner suke a wannan lokacin.

Anna, wacce ke zaune a wani yanki da ke arewa maso gabashin Moscow, ta ce ta ci gaba da zaman abokantaka da Nabiev bayan sun rabu: “Mutumin kirki ne.”

Sai dai ta ce shi talaka ne kuma yana bukatar kudi cikin sauki, don haka ya rika shiga gareji yana satar kayan mota da sauran injuna don sayarwa. Haka ya samu kansa a gidan yari, inda Wagner ta dauke shi aiki.

Tabbatar da mutuwar fursunonin a rukunin da kungiyar mayakan Wagner ke gudanarwa na iya zama da matukar wahala. Lokacin da Anna ta je ofishin daukar aikin soja na yankin su, sun ce ba su da wani labari Nabiev.

A tattare da rashin tabbas , rashin tabbatarwa a hukumance game da mutuwa a lokacin yaki na iya kawo cikas wurin albashi ko diyya daga bangaren ‘yan uwa.

Anna ta shaida wa BBC cewa “Ina so in san yana raye ko ya mutu. Bayan haka, in ban da maganar da na yi da ku, ba ni da wani bayani.” “Ina so in karɓi lambobin yabonsa, ko don in rika tunawa da shi – wannan mutum ne da nake kauna.”

‘Sojojin ko-ta-kwana miliyan 25’

Dokta Jack Watling, masani kan yakin kasa na Rasha ya ce Rasha ta yi imanin idan za ta iya dagewa a yakin da ta ke yi, kuma goyon bayan da kasashen yamma ke ba Ukraine za ta wargaje.

Idan Ukraine za ta iya keta matakan tsaron Rasha a cikin shirin tunkarar da ta dade tana shirin kaiwa, sojojin da ba su da kwarewa za su iya fuskantar “gaggarumar matsala”, in ji shi.

Sai dai duk abin da ya faru, Dr Watling ya ce da wuya Rasha za ta rasa ma’aikata, yana mai nuni da cewa ministan tsaron kasar Sergei Shoigu kan yunkurin tattara farar hula a kasar. “Lokacin da ya ce, ‘Ina da mutane miliyan 25’ a ajiye, ba wasa ba ne. da gaske yake yi kan manufarsa.”

Hakan na nufin ma’aikatan BBC za su ci gaba da samun sakonni na kirga Rashawan da suka mutu, daga mata irin su Vera da ke Irkutsk, wadda ta shafe tsawon watanni tana kokarin gano abin da ya faru da dan uwanta, bayan da aka yada jita-jitar mutuwarsa a wani rukunin mayakan Wagner.

“Ba mu san inda za mu gudu ba, ko inda za mu nemi taimako,” in ji ta. “Mu na fuskantar bala’i. Ta yaya za mu kai ga gaskiya?”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here