Ronaldo ya buga wa Portugal wasa na 199

0
84

Portugal ta ci gaba da saka kaimi a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da Jamus za ta karbi bakunci wato Euro 2024.

Ranar Asabar Portugal ta doke Bosnia And Herzegovina 3-0 a wasa na uku-uku a cikin rukuni na 10.

Daf da hutu Bernardo Silva ya ci wa Portugal kwallo, bayan da suka koma zagaye na biyu ne Bruno Fernandes ya kara ta biyu, sannan ya ci ta uku.

Cristiano Ronaldo ya buga karawar, wadda ita ce ta 199 da ya yi wa Portugal tamaula.

Tsohon dan wasan Real Madrid da Juventus da kuma Manchester United ya ci kwallo a wasan da suka yi a Estadio da Luz, amma aka soke da cewar an yi satar gida.

Da wannan sakamakon Porugal ta ci gaba da jan ragamar teburi na 10, bayan da ta lashe dukkan karawa uku da ta buga kawo yanzu.

Ronaldo mai shekara 38, da ke taka leda a Al Nassr ya ci wa Portugal kwallo hudu a wasa biyu da ya buga wa ƙasar cikin watan Maris a karawar neman shiga Euro 2024.

Bosnia-Herzegovina tana ta huÉ—un teburi da tazarar maki huÉ—u tsakaninta da ta biyu Slovakia.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here