Tasirin sabuwar dokar lantarki da shugaba Tinubu ya saka wa hannu

0
148

Gwamnatin Nijeriya ta amince da wata sabuwar doka wadda za ta bayar da dama ga gwamnatocin jihohi da kuma daidaikun jama’a su samar da kuma rarraba wutar lantarki.

Kudurin dokar, wanda Shugaba Bola Tinubu ya saka wa hannu a ranar 9 ga watan Yuni, na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Nijeriya sama da mutum miliyan 200 ke fama da matsalar wutar lantarki.

“Wannan rage karfin iko ne,” kamar yadda Shugaba Tinubu ya bayyana a lokacin da yake magana kan sabuwar dokar.

“Gudunmawar da muke bayarwa wurin ayyukan ci-gaba kuke so, kuma za mu ci gaba da bin hanyoyin da za mu taimaki mutanenmu.”

Dakta Ibrahim Danbatta, masani kan harkar makamashi a Nijeriya, ya ce wannan dokar za ta kawo sauyi kan harkokin lantarki.

“Wannan dokar za ta kara fadada bangaren wutar lantarki,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Kafin lokacin da aka aiwatar da wannan sabuwar dokar, kamfanin rarraba wutar lantarki na TCN baki daya yana karkashin gwamnatin tarayyar Nijeriya.

Tarihin sauyin

Sabuwar dokar ta kasance sakamakon sauye-sauyen da aka yi ta yi daga lokaci zuwa lokaci kan fannin makamashi a kasar da ta fi kowace karfin tattalin arziki a Afirka.

Kafin a samu wannan sauyin, dakon wutar lantarki da rarraba ta ya rataya ne a wuyan hukumar NEPA.

An rantsar da Shugaba Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu kuma ya yi alkawarin inganta ababen more rayuwa a Nijeriya. Hoto/Reuters

An karkasa NEPA zuwa kamfanoni da dama a karkashin Power Holding Company of Nigeria wato PHCN a lokacin da dokar sauyi ga wutar lantarki ta soma aiki a 2005 a lokacin gwamnatin Olusegun Obasanjo.

Wadannan kamfanonin sun kunshi kamfanoni shida masu samar da wutar lantarkin wadanda ake kira “gencos”, sai kamfani daya na dakon wutar lantarki wanda ake kira “TCN” da kuma kamfanonin rarraba wutar lantarki 11 wadanda ake kira “discos.

Duk a cikin sauye-sauye ga bangaren wutar lantarki a karkashin mulki tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan, gwamnatin kasar ta rusa kamfanoni shida na samar da lantarki inda ta sayar da kashi 60 cikin 100 na mallakarsu ga kamfanonin rarraba lantarki 11 na kasar.

Duk da wannan sauyin da aka yi, a karshe dai har yanzu wutar lantarkin da kasar ke da ita ba ta wuce megawatss 4,000 ba.

A shekarar 2021, gwamnatin Nijeriya a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari ta saka hannu kan wata yarjejeniya ta shekara shida da kamfanin Siemens AG domin kara yawan wutar da Nijeriya ke samu zuwa megawatts 11,000 zuwa 2023. Sai dai duk da haka wutar ba ta wuce megawatts 4000 ba.

Tanadin doka

Dokar wutar lantarki ta 2023 za ta bai wa jihohin Nijeriya 36 damar bai wa kamfanoni masu zaman kansu da kuma jama’a lasisin samar da wutar lantarki da dakonta da kuma rarraba ta.

Dokar ta tanadi cewa wadanda za a ba lasisin za su bi ka’idojin hukumar da ke sa ido ido kan harkokin wutar lantarki NERC kan batun adadin makamashin da ake bukatar su tanada.

Mutane da dama a Nijeriya sun dogara ne kan amfani da janareto domin samun lantarki saboda yawan dauke wuta. Hoto/Reuters

Kamfanoni ko jama’a za su iya samar da lantarkin da ta kai megawatt 1 ba tare da lasisin yin haka ba daga hukumar NERC ko kuma gwamnatin jiha.

Abin da ake so shi ne dakon wutar lantarki wanda a baya kamfanin TCN ne kadai ke iya yin shi ya zamana cewa wasu ma za su iya yi.

Sai dai dokar ba ta bayar da damar yin dakon wutar lantarki tsakanin jiha da jiha ba ko tsakanin jama’a. Har sai jiha ta samar da dokoki kan wutar lantarkinta, hukumar ta NERC za ta ci gaba da sa ido kan bangaren lantarkinta.

Tasirin wannan doka

Sakamakon yadda abubuwa ke tafiya a kasar, idan wannan doka ta soma aiki za ta yi tasiri matuka ga tattalin arzikin kasar wanda shi ne mafi girma a Afirka.

Akwai masu kananan sana’o’i da dama da za su amfana idan aka samu wadatacciyar wutar lantarki a Nijeriya. Hoto/Reuters

Daya daga cikin masanan na ganin cewa sabuwar dokar za ta kawo alkhairan da ke tattare da kasuwanci maras shinge.

“Wannan zai kawo karin ‘yan kasuwa wadanda za su kara zuba jari ta bangaren rarraba lantarkin haka kuma za a kara samun ingantacciyar wutar lantarki a Nijeriya,” kamar yadda Ibrahim ya shaida wa TRT Afrika.

“Idan ana batun farashi, za a samu gasa. Kudin wuta zai ragu, sakamakon karin wuraren da ke samar da lantarkin.”

Haka kuma ana sa ran wannan dokar za ta kara samar da aikin yi a Nijeriya, “Idan aka dubi bangaren samar da aikin yi, idan aka samu karin wutar lantarki, za a bude karin masana’antu.

Mutane za su samu karin ayyuka. Za a samu sabbin kamfanoni,” in ji Ibrahim.

Akwai sana’o’i da dama a Nijeriya da sun dogara ne kan wutar lantarki. Hoto/Reuters

Ya kuma ce wannan sabuwar dokar wata dama ce ga kamfanonin da ke samarwa da sayarwa da amfani da motoci da kekuna da babura masu lantarki domin samun sauki bayan cire tallafin man fetur.

“Kiran da nake yi shi ne a yi sauri a aiwatar da wannan doka domin ‘yan Nijeriya su soma amfana. Shugaba kasa ya kammala na shi.

Yanzu nauyin ya koma kan kamfanoni da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa an aiwatar da dokar ba tare da bata lokaci ba,” in ji Ibrahim.

Yanzu abin jira a gani shi ne irin tasirin da wannan sabuwar dokar za ta yi kan kokarin da Nijeriya ke yi na samun wutar lantarki mai dorewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here