Akalla mutum daya ne aka ruwaito ya mutu yayin da mutane hudu suka samu raunuka sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye rukunin gidaje na Trademore da ke unguwar Lugbe a Abuja ranar Juma’a.
Wani shaidan gani da ido Williams Joe, wanda ya zanta da LEADERSHIP bayan faruwar lamarin, ya ce ambaliyar ta tafi da wani direban mota kirar Peugeot, wanda aka ce ya mutu yayin da aka ceto wasu hudu.
Da yake karin bayani, Ezekiel Manzo na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ya ce an tura ma’aikatan hukumar domin su taimaka wajen dakile lamarin.
Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike da ceto a yankin Lugbe inda wani direban Peugeot kirar 406 mai lamba YLA 681 FS ya nutse a cikin ruwa kuma har yanzu ba a gan shi ba.
Sai dai ya ce an ceto mutane hudu kuma suna cikin koshin lafiya yayin da ake ci gaba da neman direban motar.
Baya ga NEMA, sauran masu ruwa da tsaki da suka halarci wurin da lamarin ya faru sun hada da hukumar kashe gobara ta birnin tarayya (FEMA) da ma’aikatar kula da muhalli ta tarayya.
A shekarar da ta gabata, Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta amince da rushe wasu gine-ginen da suka toshe hanyar ruwa.
Ministan babban birnin tarayya, Mohammed Bello, ya amince da rushe wasu gidaje 23 da aka yi ba bisa ka’ida ba.