Hanyoyi 7 da Man Kade yake gyara fatar jikin Mace

0
113

Kadanya wata bishiya ce da ta ke samar da ‘ya’ya koraye ma su zaki. Kwarai kuwa ‘ya’yan kadanya korra ne ko da sun nuna. Daga ‘ya’yan ne ake samar da man kadanya bayan an sarrafa su.

Wasu mutanen na kiran sa man kade, yayin da wasu ke kiran sa da man kadanya. Ko da wanne suna ka san shi, ba shakka man kadanya na da matukar amfani wajen inganta lafiyar dan-adam.

Tun zamani mai tsawo da ya shude ake amfani da man kadanya wajen samar da magungunan kan wasu matsalolin lafiya musamman matsalolin da su ka shafi fata saboda man kadanya na kunshe da sinadarai da dama da su ka hada da sanadaran Bitamin A, Bitamin E, Calcium da sauran su.

Daga cikin amfanin man kadanya, akwai maganin kurajen fuska da sanya laushin fata da maganin kyasbi, hakanan ana amfani da man kadanya wajen maganin fason kafa da bushewar fata, da dai sauran amfani da man kadanya ke samar wa dan adam.

Ba tare da bata lokaci ba, za mu kawo wasu daga cikin amfanin man kadanya wajen inganta lafiyarmu.

Man kadanya na maganin kyasbi; Hakanan ana amfani da man kadanya don maganin kyasbi. Idan mutum zai hada maganin kyasbi da man kadanya, sai ya samu man sandal da man ‘labender’ ya zuba cikin man kadanya sannan ya kwaba sosai sannan ya samu mazubinsa mai kyau kuma mai murfi ya zuba wannan hadin ya adana.

  1. Yadda za’ayi amfani da shi, shine, ya mayar da wannan hadin manmnyka tamkar man shafawasa, ma’ana zai ke yin amfani da wannan hadin a kullum har tsawon watanni shida. Idan Allah Ya so za a dace.
  1. 1. Amfanin man kadanya wajen maganin fason kafa; Ana amfani da man kadanya sabuda maganin fason kafa. Don samun wannan amfani na man kadanya, mutum zai yi takidin mansa mai kyau, idan dare ya yi kafin ya kwanta, sai ya goge kafarsa sannan ya shafe ta da man kadanya, sai ya sanya kafar cikin leda sannan ya sanya cikin safa, idan gari ya waye sai ya cire ya wanke. Haka zai juri yi musamman idan a lokacin hunturu ne, da sannu zai ga abin mamaki.

2. Man kadanya na maganin kyasbi; Hakanan ana amfani da man kadanya don maganin kyasbi. Idan mutum zai hada maganin kyasbi da man kadanya, sai ya samu man sandal da man ‘labender’ ya zuba cikin man kadanya sannan ya kwaba sosai sannan ya samu mazubinsa mai kyau kuma mai murfi ya zuba wannan hadin ya adana.

Yadda zai yi amfani da shi, shine, ya mayar da wannan hadin manmnyka tamkar man shafawasa, ma’ana zai ke yin amfani da wannan hadin a kullum har tsawon watanni shida. Idan Allah Ya so za a dace.

  1. 3. Ana amfani da man kadanya don laushin fata; Ga wanda ya ke son fatarsa ta kasance mai laushi, shin mace ce ko namiji sai ya yawaita shafa man kadanya a duk ilahirin jikinsa bayan ya/ta yi wanka. Ba shakka yin hakan na sanya laushin fata.

4. Man kadanya na rigafika wasu cutukan fata; An samu sahihin bayani game da yadda man kadanya ke yin riga-kafin wasu cutukan fata. Idan mutum na yawan amfani da man kadanya zai samu kariya daga kamuwa daga wasu cutukan fata. Idan ya so zai yi amfani da man kadanya kamar yadda mu ka ambata a lamba ta 3 da ke sama.

5. Man kadanya na maganin gautsin fata; Wasu mutanen Allah Ya jarrabe su da gautsin fata. Da zarar fatarsu ta sha wahala ba wuya ta samu lahani, to ma su fama da irin wannan matsala ta gautsin fata na iya amfani da man kadanya don samun waraka.

Duk mai fama da wannan matsala ya samu man kwakwa da man zaitun da kuma man ‘almond’ ya hada su ukun da man kadanya ya kwaba su, ya tabbatar sun kwabu sosai, sai ya zuba a cikin mazubinsa mai kyau kuma mai murfi ya adana. Wannan hadin zai rika shafawa a dukkan jikinsa. Don samun cikakkiyar fa’ida sai ya mayar da man kadanya matsayin man shafawarsa kowanne lokacin idan ya fito daga wanka.

6. Man kadanya na maganin bushewar labe; A samu zuma da man zaitun sannan sai a zuba a kan man kadanya a kwaba sosai. Sannan a sa a wuri mai sanyi . Sai a rika shafawa a labban baki a kullum za a samu sauki.

7. Ana amfani da man kadanya don gyaran gashi; yawaita Kitso da man kadanya na magance wasu cutukan fatar kai kamar, makero sannan yana sanya gashi laushi da tsayi da kuma sulbi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here