Gwamnan Kano zai mayar da ginin shatale-talen da ya rusa

0
196

Gwamnnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce zai mayar da ginin shatale-talen ƙofar gidan gwamnati da ya rusa, zuwa Na’ibawa dake gefen garin Kano.

Kakakin gwamnan, Hisham Habib ya sanar da cewa gwamnan da kansa ya kai matar da ta zana ginin, Kaltume Gana zuwa in da za a sake sabon ginin.

Gwamnan ya ce  wurin ya dace da ginin kasancewar ya na bayan gari kuma ba zai haifar da irin ƙalubalen da ya haifar a baya ba.

A baya dai, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce  ɗora ginin a shatale-talen gidan gwamnati ya haddasa cunkoson ababen hawa, tare da barazana ga tsaro.

A na ta ɓangaren, mai zanen, Kaltume Gana ta  godewa gwamnan bisa alkinta wanda aka yi shi domin tunawa da cikar jihar Kano shekaru 50 da kafuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here