Tinubu ya yi wa Musulman Najeriya Barka da Sallah

0
132

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga al’ummar Musulmi su yi koyi da dabi’un Annabi Ibrahim, musamman cikakken miƙa wuya ga Allah da juriya da haƙuri da rashin son kai da soyayya da kuma tausayawa.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ya fitar a wani ɓangare na murnar bikin Babbar Sallah bana.

Yayin da yake amincewa da ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta, Shugaba Tinubu ya bai wa ‘yan Najeriya tabbacin samar da hanyoyin magance matsalolin rayuwa.

Sanarwar ta ce “Dole ne mu gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya ba mu damar halartar wata Sallar Idi”.

“Yayin da muka shagala da farin ciki na wannan lokaci muna murna, kamata ya yi kuma mu dage mu tuna da ƴan baya”

“Ɗaya daga cikin ayyuka mafi girma da aka rubuta a tarihi na misali mai kyau akwai sadaukarwar da Annabi Ibrahim ya yi da ɗansa Ismail ga Allah Mahalicci.”

“Hanya mafi kyawu da za mu iya fito da wannan misali, ita ce yin koyi da wannan darasi a wajen al’ummar ƙasarmu da kuma ayyukanmu.”

“A halin yanzu, ƙasarmu na fama da ƙkalubale iri daban-daban musamman ma taɓarɓarewar tattalin arziƙinmu da kuma taɓarɓarewar tsaro.”

“Mun fara neman hanyar magance matsalolin ta hanyar shawarwarin da muka yanke kawo yanzu, don gyara tattalin arziƙinmu da kuma kawar da duk wani cikas ga bunƙasar Najeriya.”

Shugaban Najeriya ya kuma yi wa al’ummar ƙasar fatan Barka da Sallah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here