Da Buhari ya cire tallafin mai da Tinubu bai zama shugaban kasa ba — Garba Shehu

0
111

Garba Shehu, kakakin tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya ce da Buhari ya sanya hannu kan dokar cire tallafin mai da yanzu shugaba Bola Ahmed Tinubu bai zama shugaban kasa ba.

Shehu, ya wallafa hakan ne a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana dalilin da suka sanya Buhari bai sanya hannu kan dokar ba, da kuma yadda cire tallafin da Tinubu ya yi tun farkon hawansa mulki.

Lamarin ya sanya wasu na tambayar me ya sa Buhari bai cire tallafin ba shekarun da ya kwashe a mulki.

Garba Shehu ya ce tabbas da APC ta fadi a zaben 2023 da Buhari ya cire tallafin man.

Ya ce, ya amince zai yi bayanin ne domin jama’a na tambaya kan cire tallafin da neman bayanin kan mene ne ya hana Buhari sanya hannun tare da muhawarar da suka biyo bayan sausa fasalin kudi.

Ya ce kamata ya yi jam’iyya ta fito ta ba da amsa kan tambayoyin amma tilas dai ya sanya su fito su ce wani abu.

“Tabbas gwamnatin Tinubu da Shettima ta yi abun a yaba na cire tallafin mai. Mun yi imanin janye tallafin mai ba don shugaban kasa ne kawai ko don muradin kansa ba. Lamari ne da ya shafi al’ummar kasa.”

Ya ce batun janye tallafin mai da sauya takardun kudi lamari ne da suka janyo muhawara amma sai gwamnatin Buhari ta jingine batun janye tallafin mai zuwa lokacin da ya dace domin lamura su tafi daidai.

Ya kara da cewa lokacin da abubuwa suka yunkuro a lokacin zaben 2023 da gwamnatin Buhari ta dage kan cire tallafin mai da ‘yan kasa sun yi hannun riga da APC ta hanyar da za su kaurace wa zabar jam’iyyar.

“Amma sai muka yi la’akari da siyasarmu. Sai gwamnatin Buhari ta jingine batun cire tallafin mai domin jam’iyyar APC ta samunasara a zabe. Kuma hakan ya taimaka har aka samu nasara.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here