Liverpool za ta yi gogayya da Madrid kan Mbappe, Arsenal ka iya rasa Rice

0
127

Liverpool ta shirya gogayya da Real Madrid a kan Kylian Mbappe, inda za ta taya shi sama da yuro miliyan 300, in ji wakilin Fifa Marco Kirdemir. (Marca)

Harry Kane, na son tafiya Bayern Munich, to amma ana ganin tayin da kungiyar ta Jamus ta yi na farko na fam miliyan 60 da sauran tsarabe-tsarabe a kan kyaftin din na Ingila ya yi kadan sosai, don haka akwai bukatar ta biya akalla fam miliyan 100 kafin ta raba shi da Tottenham. (Guardian)

Arsenal ta yi tayi na uku a kan Declan Rice, bayan da tun da farko ta saya dan wasan na West Ham fam miliyan 100 da kuma wata karin fam miliyan 5 ta tsarabe-tsarabe. (Athletic )

Mai tsaron ragar Sifaniya David de Gea, ya kulla yarjejeniyar tsawaita zamansa a Manchester United amma kuma kungiyar ta sauya shawara, inda ta rage masa albashi. (Athletic)

Inter Milan za ta kara yunkurin neman aron Romelu Lukaku, tare da zabin sayen dan wasan na Chelsea a kan fam miliyan 25.8 a karshen kaka.

Arsenal na dab da cimma cinikin dan bayan Ajax da Netherlands Jurrien Timber, da kuma dan gaban Chelsea na Jamus Kai Havertz. (Sky Sports)

Har yanzu Manchester United na sha’awar sayen Frenkie de Jong na Barcelona , wanda Bayern Munich ita ma take so. (90min)

West Ham na tattaunawa da Juventus domin saye dan wasan tsakiya na Switzerland Denis Zakaria, wanda ya yi zaman aro a kakar da ta gabata a Chelsea. (Sky Italia)

Har yanzu Brighton ba ta samu wani tayi ba a kan dan wasanta na tsakiya na Ecuador Moises Caicedo, mai shekara 21, yayin da ita kuma ta zaku a kan Mohammed Kudus, dan Ghana da ke Ajax. (Talksport)

Liverpool da Newcastle United na daga kungiyoyin Premier da ke harin dan gaban Juventus Federico Chiesa, na Italiya wanda aka yi wa kiyasi fam miliyan 51. (Corriere dello Sport)

Leeds United na sha’awar dan bayan Liverpool Nat Phillips. (Athletic)

Real Madrid na duba yuwuwar sayen dan wasan tsakiya na Fenerbahce Arda Guler wanda farashinsa shi ne yuro miliyan 17.5 to amma kamashon da aka kara a kan kudin matashin mai shekara 18 na neman rikirkita cinikin. (ESPN)

Everton ta yi watsi da tayin fam miliyan 4 da Ipswich Town ta yi wa dan wasanta Ellis Simms. (Football Insider)

Tsohon dan wasan tsakiya na Ingila Jesse Lingard, na nazari kan makomarsa kuma bai yanke kauna kan tafiya Saudiyya ba, bayan da ya bar Nottingham Forest. (Sky Sports)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here