Sakon Shugaba Tinubu na sallah ga ‘yan Nijeriya

0
121

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce shi da tawagarsa suna aiki ba dare ba rana don ganin sun shawo kan matsalolin da ke addabar kasar.

Ya fadi hakan ne a sanarwar da ya fitar mai dauke da sakonsa na Babbar Sallah ga al’ummar Nijeriya.

A yau Laraba ne ake gudanar da bikin Sallar Layya a fadin duniya, inda a Nijeriya ma ake hutun ma’aikata na kwana biyu na sallar.

Ga dai cikakken sakon sallar da shugaban kasar ya bayyana a sanarwar.

1. Dole mu gode wa Allah da Ya sa muka sake ganin wata sallar lafiya. Kuma a yayin da muke jin dadin bukukuwan sallar ya kamata mu ringa tuna wadanda ba su da irin gatan da muke da shi.

2. A yayin da muke kawo karshen ibadun da muka shafe kwana goma na watan Musulunci na Dhul Hijjah muna yi, Sallar Layya tana hada kawunanmu a matsayinmu na Musulmai don nuna tausayi da jinkai ga dukkan bil adama.

3. Sallar Layya wani lokaci ne na mika wuya da yin biyayya ga Allah (SWT) kamar yadda Annabi Ibrahim ya yi.

4. Babu wani aiki da aka taba samu a tarihi da ya kai misalin na Annabi Ibrahim da ya sadaukar da dansa Annabi Isma’il don yin hadaya da shi kamar yadda Allah Ya umarce shi.

5. Hanya mafi kyau da za mu gwada wannan misalin shi ne na yadda za mu yi mu’amala mai kyau da ‘yan kasarmu da kuma aiki tukuru ga kasarmu abar sonmu.

6. Dole mu yi koyi da wadannan abubuwa na rayuwar Annabi Ibrahim, wato mika wuya ga Allah da hakuri da jimiri da jajircewa da rashin son kai da soyayya da kuma tausayi.

7. A wannan lokaci, mu yi kokari mu zage dantse wajen aikata ayyukan alheri da kyautatawa ‘yan uwanmu Musulmai da taimakon marasa karfi a cikin al’ummominmu. Idan muka yi haka, to mun nuna halayya masu kyau na imaninmu.

8. A wannan lokaci, kasarmu na fuskantar wasu matsaloli musamman na matsin tattalin arziki da matsalolin tsaro. Duk da na tabbatar wadannan abubuwa na faruwa, to ina son tabbatar muku da cewa ba su fi karfinmu ba.

9. Ina aiki ba dare ba rana ni da tawagata don samo mafita. Zuwa yanzu mun fara daukar matakai don sauya fasalin tattalin arzikinmu da kawar da duk wani abu da ke zama cikas wajen kawo ci-gaba.

10. A yayin da muke fuskantar matsalolin nan na yanzu, dole mu fuskanci abin da ke gabanmu da sabunta fata da karfin gwiwar cewa gobenmu za ta yi kyau da armashi.

Ina yi wa kowa Barka da Sallah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here