Akalla mutane miliyan 6 na neman agajin gaggawa a arewa maso gabashin Najeriya – MDD

0
190

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane miliyan 6 ne ke bukatar taimakon gaggawa a arewa maso gabashin Najeriya, tana mai kashedin cewa idan ba a dauki matakan gaggawa ba matsalar jinkai za ta ta’azzara  yankin da ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi suka daidaita.

Shugaban hukumar jinkai ta majalisar, Matthias Schmale, a yayin jawabinsa ga wani taron manema labarai a Geneva ya ce dole ne a tashi tsaye kada yanayin da ake ciki a arewa maso gabashin Najeriya ya munana, yana mai cewa mutane kimanin miliyan 4 da dubu dari 3 na fuskantar  matsalar matsanacin yunwa a jihohin   Borno, Adamawa da Yobe.

Tun daga shekarar 2009 ne aka shiga mummunar bata kashi tsakanin sojin Najeriya da kungiyoyin ‘yan ta’adda da suka hada da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriyar.

An kiyasta cewa sama da mutane dubu 40 ne aka kashe a wannan rikici na ta’addanci ya zuwa yanzu, kuma mutane miliyan 2 suka daidaita, abin da ke nuni da daya daga cikin munanan matsalar jinkai a cikin karni na 21.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here