Hajjin 2023: Yadda ta kaya a ranar farko ta jifan Shaidan

0
182

Dubun-dubatar mahajjata ne suka yi cincirindo a wajen jifan Shaidan na ranar farko bayan sauka daga Arafat a Hajjin bana, mafi girma tun bayan annobar cutar korona.

Tun da asubahin ranar Laraba mahajjata suka dinga tururuwar tafiya Jamra bayan yada zango a Muzdalifa bayan sauka Arafat, inda suka jefi wurare uku da ke jamrar.

Daga nan wasu daga cikin mahajjatan sun wuce birnin Makkah inda suka gabatar da Dawafil Ifada na ranar sallah, yayin da wasu kuma suka zabi komawa masaukansu a Mina, da niyyar sauke dawafin bayan kammala zaman Minan.

An yi tsananin zafi a ranakun Talata na Arafat da Laraba na jifa inda yanayin ya kai digiri 48 a ma’aunin salshiyas.

Fiye da mahajjata miliyan daya da dubu 800 ne, akasarinsu daga kasashen waje, suka samu damar gudanar da Aikin Hajjin, wanda aka dage dokokin kullen korona a karon farko tun bayan Hajjin 2019.

Sai dai yawan mutanen da suka halarci Aikin Hajjin banan bai kai yadda aka zata ba da farko, inda aka sa ran yawan mahajjatan zai fi na shekarar 2019.

Aikin Hajji na daga cikin manyan hanyoyin samun kudaden shiga na Saudiyya, wacce take kokarin fadada hanyoyin samun kudin shiga baya ga arzikin man fetur da ta dogara da shi, ciki har da mayar da hankali kan yawon bude ido.

Jifan Shaidan din shi ne aiki na farko daga cikin ranakun Sallar Layya, inda a ranar da ake na farkon ne Musulmai kuma a fadin duniya ke yanka dabbobin layyarsu.

Ana fara jifan Shaidan ne daga kan babban ginin, inda ake amfani da duwatsu bakwai ana jefawa daya bayan daya.

A bana, hukumomi sun ce tafiyar mahajjatan daga Arafa zuwa Muzdalifa har zuwa wajen Mina duk sun kasance cikin tsari, ta yadda ba a samu cunkoso ba a hanyar Jamrat Al-Aqaba din, saboda matakan da aka dauka.

Kusan alhazai 300,000 ne ke iya yin jifan Shaidan a lokaci guda cikin awa daya. An jibge jami’an tsaro da na lafiya da ‘yan sa-kai a kewayen babbar gadar zuwa Jamrat.

An ga yadda jami’an tsaro suka dinga tsara yadda kai kawon mutanen ke kasancewa a yayin shiga da fita daga yankin wajen jifan.

Wasu na’urori masu kama da shawar wanka da ke fesa ruwa sun taimaka kwarai wajen rage tsananin zafin rana da aka zabga.

Mambobin ‘yan sikawut sun taimaka sosai wajen tsara wucewar alhazai ta kofofin shiga da fita da kuma nuna musu hanyar komawa masaukansu a Mina.

Zirga-zirgar alhazan ta tafi kamar yadda aka tsara. Mahajjatan suna iya duba lokutan da aka ware musu na yin jifan Shaidand din a kan manhajar Nusuk a wayoyinsu na komai da ruwanka.

A bana, manhajar Nusuk ta sanya tsawon lokacin da zai iya daukar mahajjata yin jifan Shaidan.

Ma’aikatar Lafiya ta samar da likitoci da ma’aikatan jinya fiye da 32,000 a asibitoci 32 da cibiyoyin lafiya 140 don kula da majinyata.

Ma’aikatan lafiyan na cikin shirin ba da taimakon gaggawa ga wadanda zafi ya sumar da su ko suka fita hayyacinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here