An sa albashin Naira miliyan 104 ga mai son aikin kula da kare

0
131

Wani karin magana na Turawa na cewa “Karen saraki shi ma sarki ne a cikin karnuka.”

Kuma ga alama an kusa kwata haka a zahiri a kasar Ingila inda kan batun kare aka kusan yin hargitsi a tsakanin masu sana’ar kula da lafiyar dabbobi.

Wani kamfanin daukar ma’aikata mai suna Fairfax and Kessington a Ingila ne ya fitar sanarwar daukar aikin kula da wasu karnuka a kan albashi Dala 127 (kimanin Naira miliyan 104) a shekara.

Sanarwar ta ce, aikin da mai kula da karen zai yi shi ne zai zauna da masu karen a inda zai kula da karnukan ta fuskar kula da lafiyarsu da kiyaye su, baya ga kula da ci da shansu da mosta jikinsu da kai su ganin likitansu da duk abin da zai su yi nihsadi da walwala.

Haka kuma wanda aka dauka aikin zai kasance dan rakiyarsu a duk wata tafiya da za su yi a ciki da wajen kasar yana mai tabbatar da jin dadinsu da koshin lafiyarsu a yayin tafiyar.

Kwanaki kadan da fitar da sanarwar neman wanda zai yi wannan aiki, kamfanin ya karbi takardar masu sha’awar yin aikin mutum 3,000 a shafinsa na Intanet inda ya saka sanarwar.

“Wannan ne karo na farko da muka taba fitar da irin wannan sanarwa.Wannan zunzurutun kudi ba mu taba jin irinsa ba, ko mai mukamin likitan dabbobi da kyar ya hada wannan kudi a shekara,” in ji George Dunn a hirarsa da jaridar New York Times wacce ta fara buga labarin.

Mista George Dunn ya ce dole suka cire sanarwar saboda yadda mutane ke ta tururuwar cike takardun neman aikin da yawansu ya soma kaiwa dubbai ’yan kwanaki da sa sanarwar.

Sai ya ce, sanarwar ta dada samun tagomashi ne a yayin da wasu suka sa ta a shafin sada zumunta na TikTok inda cikin lokaci kankani ta samu sama da mutum miliyan guda wadanda suka gani.

Mista George bai ce ko sun cike gurbin ko a’a ba.

Sai dai irin jan hankalin da sanarwar ta yi, idan mai kula da karen za a ba shi wannan tsugugun kudi, shi kuma karen da mai karen fa? Wannan ce tambayar da jama’a ke yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here