Ban yi nadamar rusau a Kano ba – Abba Gida-Gida

0
116
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce bai yi da-na-sanin rushe-rushen da ya gudanar a jihar ba da kuma kwace kadarorin al’umma wadanda aka mallaka ba bisa ka’ida a jihar ba.

Gwamnan ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin Sarkin Kano Alhaji Aminu Bayero da wasu hakimai a yayin da suka kai masa gaisuwar Sallah a gidan gwamnatin jihar, kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Hisham Habib ya fitar,

“Mai Martaba yana da kyau ga masarautar Kano ta san da cewa mun kudiri aniyar rusau ne domin dawo da kadarorin al’umma wadanda aka mallaka ba bisa ka’ida ba kuma za mu tabbatar duka irin wadannan kadarorin mun dawo da su saboda al’ummar Jihar Kano,” in ji shi

Tun da farko Sarkin na Kano ya ce ya kai wa gwamnan ziyara ne domin yi masa gaisuwar Sallah da kuma tabbatar masa da cewa a shirye yake ya ba shi shawarwari wadanda za su kawo ci gaba ga jihar Kano.

Sa’annan kuma sarkin ya bukaci gwamnatin Kano ta fito da sabbin tsare-tsare domin taimaka wa al’ummar jihar Kano domin rage musu radadin cire tallafin fetur.

Tun bayan hawan sabon gwamnan na Kano ya soma rushe-rushe inda ya soma da rusa gine-ginen da ke jikin filin sukuwa.

Bayan nan kuma an gudanar da rusau da dama a wuraren da suka hada da shagunan da ke jikin makarantar sakandire ta Ƙofar Nasarawa da kuma gine-ginen da ke jikin makarantun sakandire na Duka Wuya da ta Goron Dutse.

Haka kuma gwamnatin ta Kano ta rushe katafaren shataletalen da ke gaban gidan gwamnatin jihar inda ta ce ba a yi shi bisa ka’ida ba. Sai dai ta yi akawarin gina wani shataletalen makamancin wanda ta rusa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here