JAMB za ta gurfanar da matashiya a kotu kan shirga karya a sakamakon jarrabawa

0
129

Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’a ta Nijeriya JAMB ta yi barazanar kai wata matashiya kotu bayan ta gano cewa ta shirga karya a ikirarin da ta yi na samun maki 362 a jarrabawar UTME ta 2023.

A kwanakin baya ne jaridun kasar da kafafen sada zumunta suka yi ta yada labarai cewa wata daliba mai suna Ejikeme Joy Mmesoma ta yi zarra a jarrabawar JAMB inda ta ci maki 362.

Wannan ne ya sa har wasu suka soma yi mata kyauta da yunkurin daukar nauyinta don ci gaba da karatu.

Sai dai a wata sanarwa da kakakin hukumar ta JAMB Fabian Benjamin ya fitar, ya ce sakamakon jarrabawar da ake yadawa na matashiyar na bogi ne.

“Hukumar na son fayyace cewa sakamakon jarrabawa da dama da wadannan daliban suke nunawa na bogi ne. A lokuta da dama wasu daga cikin wadannan daliban sun samu maki kasa sosai da wanda suke ikirarin sun samu inda suke amfani da wata manhaja domin sauya sakamakon domin yaudarar jama’a.

“Wanda ya fi takaici daga cikinsu shi ne lamarin Miss Ejikeme Joy Mmesoma wadda ta yi ikirarin samun maki 362 a jarrabawar UTME ta 2023 inda ta samu tallafin naira miliyan uku daga Chief (Dr.) Innocent Chukwuma,” in ji Fabian Benjamin.

Fabian ya bayyana cewa sakamakon yaudarar da matashiyar ta yi, har gwamnatin Anambra ta shirya karrama ta.

Ya kuma bayyana cewa akwai ire-iren Ejikeme da dama wadanda suke fitar da sakamakon bogi. Mai magana da yawun na JAMB ya sake bayar da misali da wani matashi Atung Gerald daga Jihar Kaduna wanda ya yi ikirarin ya ci 380 a jarrabawar.

“’Yan kabilarsa har sun soma cewa akwai bukatar a yi masa karramawa ta musamman, sai kawai hukumar ta shaida musu cewa Atung ko fom din jarrabawar bai siya ba, ballanta ya zauna jarrabawar,” in ji Fabian.

Hukumar ta JAMB ta ce za ta shigar da Ejikeme kara a gaban kotu sa’annan sakamakon jarrabawarta na ainahi za ta kwace shi.

Haka kuma ta yi gargadin cewa za ta yi bincike kan masu yin sakamakon bogi na jarrabawar inda ta ce da zarar ta gano su za ta kwace sakamakonsu na ainahi da kuma mika su wurin hukumomi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here