Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce Najeriya za ta bukaci ban-ɗaki miliyan 3.9 a duk shekara domin cimma burin kawo karshen ba-haya a fili nan da shekarar 2025.
Dakta Jane Bevan, shugabar sashen kula da ruwa da tsaftar mahalli ta UNICEF, ta bayyana hakan a ranar Litinin a wajen bude taron kwanaki biyu na masu sana’ar sana’ar ban-daki karo na farko a Abuja.
Bevan ta ce yawan ban-dakuna da ake samarwa a kowace shekara a yanzu ya tsaya ne kan guda 180,000 – 200,000, tana mai bayyana hakan a matsayin wanda bai isa ba.
Ta ce taron ya zo a lokacin da ya kamata domin masu gidajen su na da muhimmanci wajen kawo karshen matsalar yin ba-haya a fili a Najeriya.
A cewarta, kamfanoni masu zaman kansu na da rawar da za su taka wajen karfafa ɓangaren tsaftar muhalli a kasar.
Bevan ta ce mutane miliyan 48 ne ke yin ba-haya a fili, yayin da miliyan 95 ba su da hanyoyin da suka dace na tsaftar muhalli.