Mun fara shawo matsalar tsaro a Najeriya – Ribadu

0
92

Babban mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkar tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya yi iƙirarin cewa rashin tsaro ya ragu cikin mako biyu bayan naɗa sabbin manyan hafsoshin tsaron kasar.

Ribadu wanda ya yi wannan furuci bayan wata ziyara da hafsoshin tsaron suka kai wa Shugaba Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja, ya ce hakan ya tabbata ne saboda ƙwararrun hannu da aka zaɓa a matasayin masu jagorantar sha’anin tsaron Najeriya.

Ya kara da cewa sun ziyarci shugaban ƙasar ne don su nuna godiya da damar da aka ba su, ta bayar da irin tasu gudunmawar wajen ci gaban ƙasa, za kuma su yi aiki tukuru waje tabbatar da ingantaccen tsaro a fadin kasar.

Ya ce shugaba Tinubu ya bayar da tabbacin cewa zai ba su cikakken goyon baya domin gudanar da ayyukansu.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai babban hafsan tsaro, Manjo Janar Christopher Musa da babban hafsan sojin ƙasa, Manjo Janar Taoreed Lagbaja da babban hafsan sojin ruwan Najeriya, Rear Admiral Emmanuel Ogalla da babban hafsan sojin sama, Air Vice Marshal Hassan Abubakar, da kuma mukaddashin babban sufeton ‘yan sanda, Kayode Egbetokun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here