Gwamnatin Kano ta yi binciken kwakwaf kan faifen Ganduje na Dala

0
134

Gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta karbi rahoton kwararru masu binciken kwakwaf game da fefen dala wanda ya nuna tsohon gwamnan jihar Abdahi Umar Ganduje na sunkumawa a aljihunsa, inda ake zargin cewa, ya karba ne a matsayin cin hanci daga  ‘yan kwangila ne.

Kawo yanzu, gwamnatin Kanon ba ta yi wa jama’a bayani ba game da sakamakon binciken da ta tattara, inda ta ce, tana kan nazartar sakamakon.

Gabanin zaben 2019 ne, wani fefen bidiyo da editan Jaridan Daily Najeriya Jafar Jafar ya wallafa, ya nuna yadda tsohon gwamnan ke karbar dalolin daga wani da ba a bayyana fuskarsa ba a faifen.

Tuni dai gwamnatin Kanon ta bude binciken da nufin tabbatar da ganin an yi hukunci kan zarge-zargen karbar cin hancin da aka ce tsohon gwamna Ganduje ya yi.

Da ma dai sabuwar gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta lashi takobin gudanar da bincike game da faifen dalar, yayin da tsohon gwamna Ganduje ke cewa, ko a jikinsa, bai damu da wannan binciken da aka kaddamar a kansa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here